✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan matashiya ya kusa jawo rikici a Saminaka

Kisan gillar da wadansu mutane da ba a gane ko su wane ne ba suka yi wa wata matashiya mai shekara 31, mai suna A’isha…

Kisan gillar da wadansu mutane da ba a gane ko su wane ne ba suka yi wa wata matashiya mai shekara 31, mai suna A’isha Aliyu a Unguwar Mangu da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, cikin dare  ranar Lahadin da ta gabata, ya so ya kawo rikici a garin.

Yayan marigayiyar Bulus Aliyu ya ce a ranar Litinin da safe da misalin karfe 8 kanen mahaifiyarsu ya kira shi a waya. “Ina zuwa gida sai na samu gawar kanwata kwance cikin jini. Nan take na tafi wajen ’yan sanda na kai rahoto, suka zo suka dauke ta, suka kai asibiti. Bayan da likita ya gwada ya tabbatar da cewa ta rasu. Kuma sun tabbatar da cewa an soke ta ce da wani abu mai tsini a wuya a wurare hudu,” inji shi.

Bulun Aliyu ya ce su biyu ne a cikin gidan, “Da mahaifiyarmu da marigayiyar  kuma kowa dakinsa daban,” inji shi.

Bulus Aliyu ya musanta labarin da ake yadawa cewa wai su ne suka kashe marigayiyar, don ta musulunta. “Akwai yayarmu Musulma. Kuma ba mu taba yin wani tunani a kanta ba. Tunda abin da ta zaba za ta yi ke nan. Amma sai muka ji labarin wadansu suna bata sunanmu cewa mu ne muka yi sanadiyar mutuwar kanwarmu. Wannan ba gaskiya ba ne. Kuma wanda duk yake bayar da irin wannan labari, Allah zai yi mana shari’a,” inji shi.

Ita ma yayar marigayiyar wadda a wurinta ne ta musulunta, mai suna Jamila Aliyu ta  ce a watan azumin bara ne marigayiyar ta  je wajen ta a Kano ta ce za ta musulunta, akwai wani yaro da take son ta aura. Ta ce nan take ta sanya aka musuluntar da ita, ta zabi sabon suna A’isha, maimakon sunanta na da Plangnan.

“Ni ce na fara shiga Musulunci a gidanmu shekara 7 da suka gabata babu abin da ya same ni. Ina zuwa da ’ya’yana gidanmu ina yin kwanaki, idan lokacin Sallah ya yi in tashi in yi Sallah, kannena suna zuwa wurina kuma babu abin da ya taba faruwa,” inji ta.

Ta ce a danginsu a can Mangu a Jihar Filato suna da Musulmi suna da Kiristoci kuma suna gudanar da komai tare ba tare da wata matsala ba.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wanan al’amari, Mai martaba Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nuna takaicinsa kan faruwar lamarin.

Ya roki Allah Ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ta waya don jin ta bakinsa, kan wannan lamari amma bai same shi ba. Amma wata majiya a Babban Ofishin ’Yan sanda na garin Saminaka, ta tabbatar wa wakilinmu cewa an tura wannan rahoto, zuwa ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna.