✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiru/Bebeji: Kotu ta bada umarnin sake yin zaben kujerar Jibrin

A yau Juma’a kotun daukaka kara da ke Kaduna, ta bada umarnin sake yin zaben kujerar dan majalisar tarayya na mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano.…

A yau Juma’a kotun daukaka kara da ke Kaduna, ta bada umarnin sake yin zaben kujerar dan majalisar tarayya na mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano. Wanda hukumar zabe ta sanar da cewa dan majalisa Abdulmumin Jibrin, ne ya lashe zaben watan Fabrairu 2019.

Kotun ta soke zaben ne bayan dan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya Aliyu Datti Yako, na jam’iyyar PDP ya kalubalanci lashe zaben Abdulmumin Jibrin.

Tun da farko dan takarar PDP ya shigar da karar gaban kotun sauraran kararrakin zabe sai kutun ta yi watsi da karar don haka ya sake shigar da karar a gaban kotun daukaka kara.