Gwamnatin Tarayya ta bude sassan da aka rufe a hanyar da ta tashi daga Kano ta bi ta Kaduna zuwa Abuja baki daya domin zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Yanzu haka dai duk hanyar mai nisan kilomita 380 da za ta kasance a bude, daga yanzu zuwa Janairun 2023.
- Yadda Buhari ya kashe wa yankin Neja Delta N220bn
- Majalisa Ta Umarci CBN Ya Kara Tsabar Kudin Da Za A Iya Cira
Daraktan Kula da Manyan Tituna da Gyare-gyare na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya, Folorunso Esan, ne ya bayyana haka a Zariya a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin hanyoyin.
“Daga Abuja zuwa Zariya, mun lura cewa babu shingaye, don haka babu shamaki ga wanda ya biyo titin daga Abuja har zuwa Kano yanzu.
“Wannan ita ce babbar hanya a dukkanin yankin Arewa maso Yamma, ko ma Arewa baki daya, don haka ba ma son samun wata matsala a wannan lokacin na bukukuwan.
“Sauran abin da da ya rage na aikin kuma, dan kwangilar zai karasa a watan Janairu.
“Don haka, yanzu, mun bude hanya don mutane su yi amfani da su.”