✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kirgar jakuna

Wani bakauye ne ya je kasuwa ya sawo jakuna guda goma, sai ya hau daya, ya kora sauran. A hanya sai ya kirga jakunan sai…

Wani bakauye ne ya je kasuwa ya sawo jakuna guda goma, sai ya hau daya, ya kora sauran. A hanya sai ya kirga jakunan sai ya ga guda tara, saboda bai kirga da wanda ya hau ba. Da ya ga haka, sai ya sauka daga jakin, ya kirga. Nan ya ga sun cika goma, sai ya hau jakin ya ci gaba da tafiya. Can gaba sai ya kara kirgawa, ya ga sun koma guda tara, domin bai hada da wanda yake kai ba. Ya gaji da kirgawa dai ya ga tara ne, sai ya sauka. Da ya sake kirgawa sai ya ga goma cif-cif, sai ya ce: “Kai bari in sauka daga jakin nan in kora su gaba daya, hankalina ya fi kwantawa!”
Daga Loliya 08162472249