Assalama alaikum, ’yan uwana ’yan Najeriya godiya tatabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa, mai komai. Ina kira ga dukkan ’yan takarar da suka samu nasarar lashe zabukan da aka gudanar a kasar nan, sani wannan mulkin wani nauyi ne babba wanda talakawansu suka daura masu da haka nake kira a garesu da su gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci domin kuwa dukkanin talakawa da ma wadanda suka zabesu da kuma wadanda ba su zabesu ba. A karshe nake masu addu’ar Allah Ya ba su ikon rikon amanar da talakawan suka dora masu.
Daga Saidu Abdullahi Damaturu, 08039517322
Taya sabon gwamnan Jihar Kano murna
Salam Edita, don Allah ka ba ni dama na taya zababben gwamnan Jihar Kano wato Abdullahi Umar Ganduje murna. Hakika Kanawa sun yi rawar gani ganin yadda sabon gwamnan baya bukatar gabatarwa saboda kokarin da gwamnatinsu ta yi wajen ayyukan raya kasa musamman irin yadda suka mayar da jihar kamar wata kasa a nahiyar Turai.
Hakika Kanawa ganau ne ba jiyau ba domin haka muke kira ga wannan sabon gwamnan daya duba irin namijin kokarin da gwamnansa ya yi domin shi ma yayi koyi da shi domin kara darajar jihar saboda shi ma ya zama abin koyi ga saura. Daga karshe nake yi masa addu’ar Allah Ya ba shi ikon cika alkawarin da ya dauka.
Daga Aminu Abdu Baka Noma Kano, 08099479880
Taya ’yan takara murna
Ina taya ’yan takarar da suka samu nasarar lashe zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jahohi da aka yi murna kuma wadanda ba su samu nasara ba, sai
su yi hakuri su rungumi kaddara ku tari gaba. Kuma ga wadanda suka samu nasara, sai su yi kokari wajen cika alkawaran da suka dauka tsakaninsu da jama’ar da zaku mulka.
Daga Abbakar Lawal Jargaba, 08097627776
Taya jama’ar Jihar Bauchi murna
Salam, Editan Aminiya ka ba ni dama na taya ’yan uwana talakawan Jihar Bauchi murnar kawo sauyi da mu kayi a kasarmu da ma jiharmu. Kayan da muka yi wa jam’iyyar PDP tunbur a Jihar Bauchi. Haka kuma ina taya sabon Gwamnan Jihar Bauchi Mai jiran gado wato Barr M.A Abubakar, murnan samun wannan nasara da yayi. Ina kira ga sabon gwamnan da ya yi wa Allah da manzonsa ya ba da dama a gudanar da zaben kananan hukumomi cikin gaskiya.
Daga Ahmadu Manager Bauchi, 08065189242.
Guguwar Sauyi : Alkawari kaya ne
kasar nan ta bai wa marada kunya a duniya, inda abin da ake tsammani na tashin-tashina a lokutan gudanar da zabe da bayan bayyana sakamakon zaben. Kodayake an samu masu kokarin tada zaune tsaye, da wadanda akace sunyi yunkurin satar kayan aikin zaben, amma abin ya ci tura, ga alamu anyi zabukan, an kammala kuma al’umma ta gamsu, sai dai abin da ba a rasa ba.
Duk da haka anyi zabe mai nagarta fiye da na wasu lokuta a baya idan aka bi biyi tarihin zaben shekara ta 2011, amma a wannan sai son barka, inda hankulla suka kar kata shi ne fatan shugaban jagoran sauyi, Allah Ya ba shi cikakkiyar dama ta aiwatar da kudurorinsa na aiki ga al’umma,
haka ’yan majalisarsa su ba shi managartan shawarwari na yadda da dama za su ce lalai an samu sauyi, daga tsanani zuwa sauki, haka gwamnonin jahohi, da dama sun samu nasarori ne da irin farin jinin su dana jagoran sauyi, suma
muna fatan ’yan majalisun jahohin nasu za su ba da shawarwarin kwarai domin duk wanda ya samu nasara ba iyawarsa ce ba, Allah ne Ya ba shi dama ya yi abin da ya dace tun kafin lokaci ya komo na idan anji dadi a bashi dama, idan kuwa sukai yadda suke so, to wadanda suka gabata sun isa buga misalai. Da fatan shugaban kasa kuma jagoran sauyi a Najeriya dama duka kasashen mu na Afirka da gwamnonin jahohi ku yi da gaske muna taya ku fatan samun sauyi managarci.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519