✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kidmas: Dan Jos da ke jan zare a kwallon kafa a Australia

Ina jiran in ga lokacin da zan buga wa Najeriya kwallo a nan gaba.

Wani matashi haifaffen garin Jos da ke Jihar Filato, Aaron Kidmas wanda yanzu yake wasan tamola a Kungiyar Davenport City Strickers da ke buga gasar Firimiya ta kasar Austireliya mai suna Tasmania yana jan zarensa a gasar.

Kidmas, dogo, kakkarfa yana haskawa ne saboda yadda yake taka leda a tsakiya kwatankwacin tsohon dan kwallon Barcelona da Manchester City, Yaya Toure.

Dan wasan tsakiyar ya fara taka leda ne a Kungiyar Kwallon Kafa ta Riverside Olympic tun yana dan shekara wanda tun a nan ake yaba baiwar tamolan da yake da ita.

Dan wasan ya bar Najeriya tare da iyayensa tun yana dan shekara hudu da haihuwa zuwa kasar Austreliya inda ya koyi wasan kwallon kafa a kasar.

Duk da cewa yana da shaidar zama dan kasashen biyu, amma zuciyarsa ta fi karkata ne ga mahaifarsa Najeriya.

Ya ce duk da nisan da ke akwai tsakanin kasashen biyu amma yana bibiyar abubuwan da suke tafiya a kasarsa ta haihuwa saboda son sa ga mahaifarsa.

“An haife ni ne a garin Jos na Jihar Filato. Ina kallon kaina a matsayin wanda ke da baiwar tamola. Garin Jos ya fitar da fitattun ’yan kwallon kafa irin su Segun Odegbami da Sama’ila Mabo da Benedict Akwuegbu.

“Mahaifina ma ya sanar da ni daga baya cewa ’yan wasa irin su Ahmed Musa da Obinna Nsofor da Ogenyi Onazi da Sunday Mba duka daga garin Jos suke,” inji shi.

Kidmas ya ce babban burinsa shi ne ya buga wa Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa wato Super Eagles.

“Ina jiran in ga lokacin da zan buga wa Najeriya kwallo a nan gaba. Ina sha’awar wata rana na buga wa Super Eagles wasan tamola,” in ji shi.