Ci gaba daga makalar da aka sanya ranar Juma’a16 ga watan Janairu
Hankalin Ladidi ya yi matukar tashi sanadiyar wadannan tambayoyi, domin ta san ko shakka babu wani al’amari mai muni ya faru da kawarta. Amma sai ta yi kamar ba ta fahimci wani abu ne ya faru ba. Kai tsaye ta shawarci Lubabatu da su je wajen malam domin samun amsoshin tambayoyin. Nan take suka sulale daga gidan bukin ba tare da kowa ya sani ba.
Malam Sa’idu malamin kirki ne kuma wanda ya san inda duniya ta sanya a gaba. Saboda haka bai yi mamakin jin dogon labarin da Lubabatu ta sanar da shi ba, kuma nan take ya hakikance a ransa cewa, Allah ne ya jarabce ta da kuma wancan saurayin, sanadiyar munanan aiyukan mutane da suke duba dare da rana ba tare da sun yi duba izuwa nasu laifin ba. Saboda haka kafin ya amsa tambayarsu, sai ya fara da cewa:” Lubabatu na tausaya maki a kan wannan hali da kika samu kanki, ina kuma ba ki shawarar ki kai zuciyarki nesa tare da dagewa wajen neman gafarar
Allah. Hakika kun aikata kuskure mai girma, da kuka bari laifukan wasu mutane suka zamar maku abin dubi, wanda ina kyautata zaton shi ya sa wannna jarrabawa ta afka muku, domin Allah Ya fahimtar da ku cewa ku ma ba kun fi karfin lamarin ba,Allah ne Yake kare ku.”
Hawayen da suka zubo daga idanuwan Lubabatu ne suka sanya malam Sa’idu katse doguwar nasihar da ya kwararo, kai tsaye sai ya shiga zuwa amsa musu tambayar da ta kawo su. ”Daga farko dai; duk yarinyar da wani namiji ya sadu da ita, to wajibi ne ta yi istibra’i kafin a daura mata aure’’ In ji Malam Sa’idu. Sai dai Ladidi ta katse shi da tambayarta ‘’Malam mene ne Istibra’i kuma?”Istibra’i wani lokaci ne da macen da aka yi zina da ita ko kuma aka yi mata fyade take dauka ba tare da an daura mata aure ba, kuma ba za ta sadu da ko wanne da namiji ba tsawon wannan lokacin har sai ta ga jinin al’adarta ya zo mata sau daya zuwa sau uku. Ana yin hakan ne domin gudun ita yarinyar kada ta je gidan wani da cikin wani. Kamar yanzu kawarki, wa yake da tabbacin cewa ciki bai shiga ba a lokacin saduwarta da wancan saurayin?’’ In ji Malam Sa’idu. Ladidi ta kau da fuskarta cike da tausayin halin da Lubabatu ke ciki ba tare da ta amsa tambayar ba.
Malam ya ci gaba da yi musu bayanin cewa; wannan auren da aka daura wa Lubabatu a yau, lalle babu shi, kuma wajibi ne a dakatar da kai ta gidan mijin har sai ta yi Istibra’i. Idan aka tabbatar ba ta da juna biyu, sai a sake daura mata aure. Idan kuma aka yi rashin sa’ar cewa ciki ya shiga, to lalle ne sai ta haihu, sannan za a yi zancen kuma aurar da ita. Malam ya kara da tabbatar musu cewa, ko da kuwa wannan din da ya kwanta da ita shi ne wanda zai aure ta, lalle Istibra’i ya zama dole.
Wannan fatawar da malam ya bayar, ta jefa Lubabatu cikin tsananin rudani da tunani! Da wane irin idanuwa al’umma za su kalle ta? Amma da ta tuna da cewar duk wanda za ka yi baki a idanuwansa, idan dai domin neman gafara ne da kuma bin dokar Allah, ba hasara ce ba. Sai ta rungumi kaddara. Ta bar wa Allah al’amarinta. Aka watse buki baram-baram ba tare da an kai amarya ba.
Za a iya samun Nasir a 08033186727
Za mu ci gaba mako na gaba