Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon za mu fara kawo muku gajeren labari mai suna ‘Kibiyar Tsautsayi’ wanda Nasir Abbas ya bada gudunmuwarsa ga filin Iyayen Giji. Ina fata za ku bi labarin sau-da-kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa. A sha karatu lafiya:
Daga Nasir Abbas Babi
Ba sai an gaya maka ba, yanayin zaman zugum din da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Alhaji Bala da matarsa Ladidi, tare da ’yarsu Zuwaira wadda ke gefe daya tamkar ruwa ya cinye ta ne, zai tabbatar maka da cewar ba lafiya ba!
“Zama hakan fa ba zai kawo wani sauyi daga wannan tsautsayi da ya same mu ba, ta yaya za a ce yarinyar nan na da juna biyu kuma har ya kai watanni biyu ba tare da mun sani ba?’’ Ladidi ce ta fadi hakan a lokacin da Alhaji Bala ya kura mata idanuwa cike da son ya dora alhakin wannan sakacin a kan ta.
Abin da Alhaji Bala bai sani ba shi ne, duk da yadda yake mamakin yadda ’yarsu Zuwaira ta aikata wannan abin kunyar, matarsa Ladidi ta fi shi yin wannan mamakin. Sai dai ita ta yi imani da maganar da ke cewa: “BABU kARFI A CIKIN YI WA ALLAH BIYAYYA, KUMA BABU DABARA A CIKIN BARIN SAbA WA ALLAH FACE DA TAIMAKON ALLAH.’’ Ta yi imani da hakan ne tun daga ranar auren wata kawarta wadda suka shaku sosai mai suna Lubabatu.
Lubabatu ta kasance yarinya mai hankali da tunani, mai ilimin addini da na zamani tare da girmama da na gaba da ita. Zan iya cewa lallai ta amsa sunanta na ’ya mace, kuma tauraruwa a cikin ’yan matan, musamman halin kamun kai da kowa ke yi mata shaidarsa. Sai dai a ranar aurenta, ta tsinci kanta a cikin halin kunci da damuwa sanadiyar azal din da ya fada kanta! Domin kuwa kwana goma kafin ranar, wani saurayi mai suna Sadau ya yi awon gaba da budurcinta, wanda ta kasance tana kariya da rayuwarta tsawon shekara 13.
Sadau da Lubabatu sukan hadu ne a makarantar da suke karatu tare, inda suke tattauna matsalolin da suka addabi al’umma na lalacewar tarbiyya. Sai dai duk da cewar dukansu mutanen kirki ne, sun dauki kansu masu cikakken tsarki. Sun manta da cewar hatta wannan haduwar tasu ta saba wa shari’a. Sai suka take laifinsu suka mayar da laifin wasu abin kallo da zargi. Wanda hakan ne ya janyo Kibiyar Tsautsayi ta illata su.
Wata rana da daddare, Sadau ya je gidansu Lubabatu domin yi mata barkar aurenta da ake shirin yi, sai aka yi rashin sa’a, shaukin rabuwa da juna ya dibe su, kafin ka ce tak, Shaidan ya kada musu gangar hilata, ba su ankara ba sai ga shi sun aikata abin da ba su shirya aikatawa ba ko da da rana daya. Dama kun san sharrin shaidan ya wuce wasa.
Za mu ci gaba
Kibiyar Tsautsayi!
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon za mu fara kawo muku gajeren labari mai suna ‘Kibiyar Tsautsayi’ wanda Nasir…