✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Keke da mota 1

Wani mai mota ne yana gudu za shi wani wuri sai kawai wani mai keke ya yi gilma masa, shi kuma ya buge shi. An…

Wani mai mota ne yana gudu za shi wani wuri sai kawai wani mai keke ya yi gilma masa, shi kuma ya buge shi. An tsaya ana cece-kuce, kawai mai keke ya ce a biya shi kekensa, mai mota ya ce shi ma haka. Da aka tafi kotu, alkali ya ji batun kowa sai ya ce: “To ina mai keken da ya buge mai mota?” Mai keke ya tashi cikin mamaki ya ce: “Yallabai inji uban waye?” Alkali ya ce: “Ku kama shi ku kai jarun, ya zagi alkali.”
Daga Tukur Ruwaya Gargaje, Zariya 08064245780