Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce mutum 10 sun rasu, wasu 500 kuma na kwance a asibiti bayan da suka sha gurbatattun kayan shaye-shaye.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce mutum 50 daga cikin wadanda aka kwantar din suna fama ne da cututtuka masu hadari ga koda.
- Gumsu Abacha: Gwamnan Yobe ya ba da sadakin zinare 24
- Hisbah ta kama samari da ’yan mata marasa azumi a Kano
- Yadda ’yan daban daji 30 suka fada tarko a Katsina
- Shin yaushe Buhari zai dawo Najeriya daga Landan?
Ya bayyana cewa, “A baya-bayan nan, Ma’aiktar Lafiya ta sanar da barkewar wata bakuwar cuta mai alaka da gurbatattun kayan sha.
“Amfani da wadannan gurbattun kayan abincin na da matukar hadari ga kodar dan adam da wasu sassan jiki.”
Don haka ya ja hankalin mazauna da su guji shan kayan shaye-sayen musamman a watan azumin Ramadan domin kauce wa mummunan sakamakon da hakan ke iya haifarwa.
Tuni dai Hukumar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Jihar Kano ta fara bi kasuwanni tana kwace kayayyakin na kara wa kayan shaye-shaye armashi.
A lokacin za gayayen, Hukumar ta gano wasu daga cikin sinadaren da wa’adin aikinsu ya kare tun akalla shekarar da ta gabata.