✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kayan kwalliyar da za su dace da fatarku

Ya kamata mata su san irin kayan kwalliyar da za su dace da fatarsu, saboda amfani da wadanda ba su dace ba za su iya…

Misalin man da za ki rika shafawaYa kamata mata su san irin kayan kwalliyar da za su dace da fatarsu, saboda amfani da wadanda ba su dace ba za su iya yi wa fatarku babbar illa.
A yau mun kawo muku shawarwari da suka shafi irin kayan kwalliyar da za ku yi amfani da su ga dukkan nau’ukan fata, wato ga fata mai gautsi ko mai maiko da marar maiko har ma da marar gautsi. Muna son ku fahimci za a iya samun wadannan kayan kwalliyar a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya na zamani.
Fata mai gautsi: A kodayaushe fata mai gautsi takan yi kanfar mai, don haka idan fatarku mai gautsi ce sai ku nemi:
•     Man ‘double-duty’ fandeshi. Wannan fandeshin na dauke da wani maiko da ke taimaka wa fata mai gautsi.
•         Kada ku rika sayan mayukan da suke dauke da sinadarin alcohol saboda wannan sinadari na bata fata mai gautsi.
•    Ya kamata ku rika shafa mai a-kai-a-kai.
Fata mai maiko: Hakan yana faruwa ne saboda yawan kiba ko gumi da ke jikinmu.
•   Don haka sai ku samu cleanser wadda ke tafiyar da datti da kuma maikon fuska, wadda kuma za ta iya kashe kwayoyin cuta da suke haifar da kurajen fuska.
•         Kada ku rika amfani da man da zai canza kalar fata ga fatar da take da maiko domin yin hakan na dada maikon fuska.
•         A sayi hodar fandeshi da za ta iya tsotse maikon fuska.
•         A rage yawan shafa fuska da rana saboda tafin hannu na dauke da nasa maikon. Kun ga idan an yi hakan zai kara maiko a fuska.
•         Kuma sai a rika yawaita canza gidan matashi don tsabta.
Fata marar maiko da gautsi: Irin wadannan fatu ba su da gautsi da kuma maiko. Za a gan su babu kuraje, kuma irin wadannan fatar na canzawa saboda yanayin wuri; ko damina ko rani ko kuma hunturu.
•         Ana sayan fandeshi da aka rubuta ‘normal skin’, misali man TRUblend da sauransu.
•         Za a iya shafa mayukan da za su sa maiko a kan irin wadannan fatu da hunturu.
•         Kuma a kasance tare da hoda a kowane lokaci, saboda idan zafi ya zo za a iya shafawa domin fatar na canzawa ne saboda yanayi.