✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kauyen Kwamfuta shi ne jigon bunkasa Kimiyyar Sadarwa a Afirka – danbatta

Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC), Farfesa Umar Garba danbatta ya ce kauyen Kwamfuta Na Najeriya shi ne jigon bunkasa…

Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC), Farfesa Umar Garba danbatta ya ce kauyen Kwamfuta Na Najeriya shi ne jigon bunkasa Kimiyyar Sadarwa na Afrika. kauyen Kwamfutar, wanda yake a Otigba Ikeja-Legas, an bayyana shi da cewa shi ne kasuwar sayar da kayan kimiyyar sadarwa mafi girma a Afrika da ke samar da kimanin Naira biliyan 1.5 a kasar nan a kullum.

Ya bayyana haka ne a yayin da ya ziyarci kungiyar Dillalan Kayan Kwamfuta Da Dangoginta Ta Najeriya (CAPDAN) da shuwagabannin kasuwar, a Legas kwanan baya. danbatta ya kara da cewa, gudunmowar da kasuwar ke bayarwa ga tattalin arziki tun daga bullowar harkokin sadarwa na zamani shekara 16 da ta gabata ya kai Dala biliyan 32.

Kamar yadda danbatta ya ce, akwai kimanin kanana da matsakaitan kamfanonin kasuwancin kayan kimiyyar sadarwa 3000 da suke gudanar da harkokinsu a kasuwar. “Saboda haka, kauyen Kwamfutar na bukatar babban tallafi domin ta samu damar ci gaba da tallafa wa tattalin arzikin kasa.”

A lokacin da yake bayyana shirin hukumar NCC na aiki da kungiyar CAPDAN, shugaban ya bayyana cewa zai sanya hannun yarjejeniyar aiki tare da kungiyar. Ya shawarci kungiyar da su magance matsalolin da ake samu na sayar da wayoyin hannu na jabu, marasa inganci, wadanda ba su samu amincewar NCC ba. A cewarsa, irin wadannan wayoyi suna da matsala kuma suna taimakawa wajen haddasa matsaloli ga kamfanonin sadarwa a kasar nan, don haka su taimaka wajen kare martabar al’ummar Najeriya. “Ina kira gare ku, da ku taimaka wajen ganin bayan irin wadannan bara-gurbin ’yan kasuwa da ke sayar da gurbatattun wayoyi.”

danbatta ya ce, a daya daga cikin hakkokin hukumarsu, za su ba membobin CAPDAN da yawa horarwa.

A yayin gabatar da jawabinsa na maraba, Shugaban kungiyar CAPDAN, Ahmed Ojikutu ya ce kasuwarsu ita ce ke samar da mafi yawa daga kayayyakin kimiyyar sadarwa a Najeriya da Afrika gaba daya. Ya kara da cewa kasuwar tasu sananna ce wajen samar da kayayyakin kwamfuta a Afrika, wacce ke samar wa dinbin matasan da suka kammala jami’a aikin yi a yankin.

Ojikutu ya tunatar da cewa harkokinsu ya wuce batun sayar da wayoyin hannu, “kasuwa ce da harkokin daban-daban ke gudana. Ana gyara, kwaskwarimar waya ko kwamfuta cikin kwarewa, domin kuwa masu gudanar da harkokin nan suna da kwarewar da ake bukata a kera na’urorin ma gaba daya. Mun yi amanna da cewa wadannan kwararru za a tallafa masu domin su ci gaba da ba da tasu gudunmowa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. A ganinmu, lokaci ya yi da za a bunkasa kasuwar nan, domin ta kasance Babbar Kasuwar Harkokin Kimiyyar Sadarwa ta Afrika.”

Shugaban na kungiyar CAPDAN ya roki shugaban NCC day a taimaka wajen daukar nauyin membonbinsu zuwa karatu a makarantar koya ilimin kwamfuta ta Digital Bridge (DBI) da kuma zuwa tarukan bita a kasashen waje da kuma girka na’urar karfafa yanayin intanet (broadband) da sauransu.