✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kauyen Gauta: Inda mahaukata 40 ke zama a daki daya

A wannan mako ne Aminiya ta ziyarci kauyen Gauta da ke Karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa, inda aka kafa wata cibiyar kula tare da…

A wannan mako ne Aminiya ta ziyarci kauyen Gauta da ke Karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa, inda aka kafa wata cibiyar kula tare da samar wa masu tabin hankali magani.

Cibiyar mai suna Musabil Herbal Centre, akwai masu tabin hankali 107, inda kuma kowane daki ke dauke da majinyata 40 da suke zaune tare ba tare da sun yi wa junansu illa ba.

A binciken da wakilinmu ya gudanar, ya gano cewa kowane lokaci a kan ga motoci da babura suna shiga da masu tabin hankali cikin cibiyar, wadanda ’yan uwansu ke kawo su don neman waraka. Ya lura da wani abu da ya bambanta cibiyar da sauran cibiyoyi da asibitotin kula da masu tabin hankali a jihar, shi ne yadda ake barin majinyatan suna cudanya da junansu, a yayin da ake ba su magani ba tare da an saka musu ankwa ko sarka ba; kamar yadda ire-iren cibiyoyin na gargajiya da na zamani ke yi. Haka kuma har zuwa lokacin da wakilinmu ya bar cibiyar, babu wani ko wata daga cikin wadanda ake jinyar da ya tada zaune-tsaye ko wani abu makamancin haka.

Wakilinmu ya lura cewa babbar hanyar da ake gane suna da tabin hankali ita ce ta irin tambayoyi da bukatu da suke gabatar wa babban daraktan cibiyar, duk lokacin da yake ziyartarsu a dakunansu. Kuma wadanda aka lura suna samun sauki cikin sauri, akan bar su su tafi wuraran ibadarsu, su kuma dawo cibiyar da kansu ba tare da sun jawo wa mahukuntan cibiyar wata matsala ba.

Wakilinmu ya kuma samu labarin cewa kimanin mutum 47 daga cikin masu tabin hankalin sun samu lafiya, an sallame su; yayin da daga bisani aka dauke su aiki a cibiyar a matsayin masu gadi da tsabtace muhalli da sauransu.

Da yake ganawa da wakilinmu, wanda ya kafa cibiyar Dokta Kabiru Mohammed, kuma Babban Daraktan cibiyar, ya ce asalinsa mutumin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja ne. Ya ce bayan ya koma garin Keffi a Jihar Nasarawa sai ya kafa cibiyar don ba da tasa gudunmawa a bangaren taimaka wa masu tabin hankali.

“Na kafa cibiyar ce kimanin shekara daya da wata uku ke nan. Na gaji sana’ar jinyar masu tabin hankali ne daga wurin mahaifina amma daga baya sai na yanke shawarar daukar kwararrun likitoci, domin taya ni aikin,” inji shi