✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar shanun Lobanta na ci gadan-gadan – Shugabannin kasuwar

  Tun daga lokacin da aka samu farraka a kasuwar shanu ta Lobanta, da ke Lobanta jihar Abiya da kuma abokan sana’ar su ’yan Mubi…

 

Tun daga lokacin da aka samu farraka a kasuwar shanu ta Lobanta, da ke Lobanta jihar Abiya da kuma abokan sana’ar su ’yan Mubi da suke tattare wuri guda suke sayar da shanu kimanin shekara 12 ke nan, inda abokan kasuwancinsu da ake kira ’yan Mubi suka kama gabansu, suka koma tsohuwar kasuwar shanu ta Okigwe, da ke Jihar Imo cikin watan da ya gabata, inda wakilinmu ya ziyarci kasuwar shanun don ganin halin da ake ciki, saboda wasu na zargin mutuwar kasuwar shanu ta Lobanta ya zo, sai ga shi labarin ba haka ya kasance ba. 

Wakilin mu ya tattauna da dattawan kasuwar da suka hada da Alhaji Muhammed Sale shugaban kasuwar shanun da kuma mataimakinsa Alhaji Ramat Adam kan kokarin da suke yi na ganin kasuwar tasu ta ci gaba da ba ta mutu ba, kamar yadda wadanda suka balle daga cikin su suke yin hasashe.
“Mu ba mu da wata matsala a kasuwar mu, kuma sai dai mu ce Alhamdulillahi ma domin ka ga duk kasuwar nan mu ne ’yan Arewa zalla, kuma mu’amala ma tsakanin mu da ’yan asalin Jihar Abiya da ma makwabtan jihohin Enugu da Imo lafiya lau. Sai in ce maka a kasuwar mu kamar ma wasu ba su fice daga cikin mu ba, ga shanu nan masu yawa sun haura guda dubu biyu, kuma wasu ma na nan tafe, don ma ba a dawo da su daga wajen kiwo ba,”inji shi.
Ya ci gaba da karyata matsalar tsaro da wadanda suka fice daga kasuwar suka ce ita ta sanya su komawa Okigwe shugaban kasuwar ya ce wannan zance ba haka yake ba.
“Sai in ce maka matsalar tsaro da suke fada ba gaskiya ba ce. Domin ka gan mu nan mu duka, kowa da ka ga ni a gidan kansa yake, kuma kafin ka shigo gari akwai jami’an tsaro. Haka ma idan za ka fita mu muna zaune nan hankali kwance; muna kasuwancin mu ba matsala, domin muna da sojoji, muna da ’yan sanda da kuma moba duk suna nan dare da rana, suna aikin su. Don haka son zuciya ne wasu suke cewa rashin tsaro ya kore su daga lobanta,” inji shi.
Shi ma Alhaji Ramat Adam, da yake tofa albarkacin bakinsa game da kasuwancinsu ya shaida wa Aminiya cewa, magana ta gaskiya idan da wadanda suka fice daga cikin su za su so gaskiya da ba su kaurace wa kasuwar ba, suka koma wani wuri.
“Tsawon shekara 11 muna kasuwanci a nan babu wata fitina muna zaune lami-lafiya da kowa, baki da ’yan asalin jiha har da makwabta ma ina kira gare su, da su dawo su ci gaba da kasuwancin su, tunda kasuwar ta su za su haifar wa kansu matsala. Domin yau wanda ya sayi saniya a can idan kudi suka makale nan zai dawo ya ci gaba da sayen saniya, ba tare da sun sani ba ka ga can kudin su sun makale nan kuma ana kunyar abiyo sawu,”inji shi.
Alhaji Magaji Dede, shi ne Sarkin Zango a kasuwar shanu ta Lobanta ya tabbtar da cewa, daukar matakin kare dukiyar duk wani wanda ya kawo shanu kasuwar da kuma mutuncinsa, kuma ya karyata zargin da wasu suke yi na cinye wa fatake kudi da wasu batagari da suka koma wata kasuwar suke yi.
“Alhamdulillahi mataki na farko shi ne koda aka sanar min nan take na sanar wa jami’an tsaro, kuma suka zo. Ka san mutum idan kana tare da shi babu abin da ba zai iya zargin ka da shi ba. Wannan duk zargi ne da ma sun yi shirin su ne na su koma wani wuri daban, shi ya sa suke bata mana suna.Kuma ba zai sanya su yi nasara ba idan ka lura yadda mu, muke a nan zaune da yadda su, suke fa ai kasan akwai bambanci. Muna zaune cikin kwanciyar hankali. Su kuma fa ? Farfaganda ce ta banza irin tasu, kuma kasuwar mu yanzu haka idan ma ba ka sani ba, ba za ka taba gane ko wasu sun balle daga cikin mu ba,” inji shi.