✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwancin aya da dabino na shirin subuce wa Katsinawa

Na sayi tiyar dabinon Naira 1800 a yau, babu mamaki gobe ya wuce haka.

Bayan rufe kan iyakokin kasar nan, farashin aya da dabino ya hauhawa. Kimanin shekara biyu ke nan kuma da alama har yanzu farashin ya ki sauka, musamman a Jihar Katsina, kamar yadda Aminiya ta fahimta.

Shugaban kungiyar masu sayar da ayar da dabino a jihar, Malam Isma’ila Ibrahim ya alakanta lamarin da dakatar da shigowa da dabino da ayar zuwa cikin Najeriya da aka yi sakamakon rufe kan iyakoki.

“To gaskiyar magana ita ce, mun fara samun tashin farashin tun lokacin da aka ce an rufe kan iyaka.

“Ka sani, muna shigowa da aya da dabino daga waje duk kuwa da noma wasu da muke yi a nan cikin gida.

“Wannan rufewar ita ta sa ya fara wannan tsada har zuwa yau don a can baya muna sayen buhu mafi tsada a lokacin kan Naira dubu 20.

“Tiya daya a lokacin bai wuce Naira dari biyar ba amma a yau, duk wanda ya ce maka ga iyakar farashin to ya fadi son ran shi kawai.

Wata matsalar ma a yanzu shi ne yadda har yanzu ba mu samun damar shigowa da shi duk kuwa da cewa an bude kan iyakokin.

“Sannan a iya saninmu, dabino ko aya ko cukwui ba sa daga cikin kayayyakin da ake haramta shigowa da su amma mu har yanzu an hana mu shigo da su,” inji shi.

Ya karyata zargin da jami’an tsaron kan iyaka ke yi cewa ana amfani da hanyar shigo da dabinon da aya ana shigowa da miyagun kwayoyi da makamai.

“Duk da cewa, kowane irin abu kake yi ba za a rasa batagari ba; jin wannan ne ya sa mu a kungiyance muka shiga bin hanyoyin tsabtace sana’ar duba da cewa, duk inda za ka ga aya ko dabino ko shi cukwui a duk fadin Najeriya, to daga nan Jihar Katsina aka fitar da shi.

“Mun yi maganar biyan duk wani haraji bayan mun tabbatar musu cewa, mun dauki duk wasu matakai na tabbatar da cewa mun tsare dokoki tare da sa ido a kan duk wani motsin kayan, amma har zuwa yau hakarmu ba cimma ruwa ba.”

Shugaban ya yi kira kira da babbar murya ga gwamnatin Jihar Katsina da ta shigo cikin batun kasuwancin nasu.

“Muddin muka bari wannan kasuwancin ya fita daga jihar ya koma wani sashe na kasar nan, to gaskiya ba karamin rashi da koma baya za a samu ta fuskar samun kudaden shiga da kuma rage zaman kashe wando a tsakanin matasanmu ba.

Aminiya ta tattaunawa da wani da ya bukaci a sakaya sunansa da ya zo sayen dabinon yin buda baki.

A cewarsa, “To wannan matsala ta tsadar wadannan kayayyakin dabinon da sauran wasu kayan marmarin sai a ce inda sabo an saba.

“Yanzu na zo na sayi tiyar dabinon Naira 1800 a yau, babu mamaki gobe ya wuce haka.

“Misali, kwallon kankanar da muka saya Naira 250 kafin azumin yau in ba ka da Naira 600 ba za ka samu irin ta ba.

“Saboda haka, nake ganin baya ga kira ga ‘yan kasuwar, ita ma gwamnati akwai rawar da za ta iya takawa, ta rika sayo irin wadannan kaya tana sayarwa tunda abu ne daga shekara sai shekara,’’ inji shi.