✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 89 na masu coronavirus a UAE sun warke

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce wadanda suka warke daga cutar coronavirus a kasar sun kai kashi 89 cikin 100. Sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar…

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce wadanda suka warke daga cutar coronavirus a kasar sun kai kashi 89 cikin 100.

Sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar sun nuna mutum 57,694 ne suka warke daga cutar daga cikin 65,186 da suka kamu.

Hakan na zuwa ne yayin da makarantu masu zaman kansu a kasar ke shirin budewa domin ci gaba da darussa da daliba a cikin aji.

Galibin dalibai ‘yan shekara hudu zuwa 11 za su koma makaranta ne a ranar 30 ga Agusta inda za a rika koyar da su dai-daya.

Bayan sati hudu sauran dalibai na gaba da su kuma za su dawo daukar darussa kai tsaye a cikin aji.

Ma’aikatar lafiyar ta ce hakan zai ba wa makarantu damar yin shiri da kuma lura da yadda kananan dalibai ke bin matakan kariya domin hana yaduwar COVID-19.

Ta ce karuwar alkaluman wadanda suka warke zuwa kashi 89 ya faru ne bayan mutum 123 sun warke wanda hakan ya kai adadin zuwa 57,694 daga cikin mutum 65,186 da suka kamu.

Zuwa yanzu mutum 364 ne cutar coronavirus ta kashe a UAE inda a baya-bayan nan ta yi ajalin mutum uku.

Rahoton karshe da ma’aikatar ta fitar ya ce mutum 210 sun kara kamuwa da cutar cikin sa’a 24.