✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 64 na yaran Jigawa suna fama da tamowa

Kashi 64 cikin 100 na kananan yaran Jihar Jigawa suna fama da ciwon yunwa wanda aka fi sani da tamowa Darakta a Hukumar Lafiya a…

Kashi 64 cikin 100 na kananan yaran Jihar Jigawa suna fama da ciwon yunwa wanda aka fi sani da tamowa

Darakta a Hukumar Lafiya a Matakin Farko, Dokta Shehu Sambo ya tabbatar da haka a hira da manema labarai a ofishinsa da ke Sakatariyar Gwamnatin Jihar.

Dokta Sambo ya ce gwamnatin jihar ta bai wa wata kungiya da suke da hadin gwiwa da ita a yaki da ciwan tamowa Naira dubu 300 don kawo musu sinadarin yaki da ciwon na tamowa daga kasar Amurka, amma yau shekara biyu babu maganin babu kudin na hada-ka da suka bayar.

Dokta Sambo ya nuna damuwarsa kan gazawar abokan huldarsu na kawo wa Jihar Jigawa sinadarin yaki da cutar.Ya ce sakamakon haka ne ya sa gwamnati ta kafa wani kwamati da za shirya gangami da zai yi yaki da cutar da kuma wani shiri da suka bullo da shi na Masaki a madadin wancan da suka shirya da kungiyar wadda ba a fadi sunanta ba suka bullo da shirin da ake gwada wa mata girke-girke da za a rika ciyar da yara da abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki.

Ya kuma nuna rashin gamsuwa da tsarin sayen sinadarin daga kasar Amurka, inda ya bayyana cewa yanzu shirin na Masaki ya samu karbuwa kuma yana biyan bukata ga yaran da suke da matsalar tamowa, saboda haka ya ce za su rungumi shirin na Masaki kawai a madadin wancan shiri.

Ya kuma nuna damuwarsa game da yadda wadansu ma’aikatan lafiya suke kyamar marasa lafiya da mata masu juna biyu yayin awon ciki a mafi yawan  asibitocin jihar, kuma  ya nuna damuwarsa kan karancin wayewar kan al’umma a jihar, musamman a kan harkokin rigakafin cutar shan inna da ciwon sankarau.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki ma’aikatan lafiya sama da 600 kuma tana da asibitoci sama da 700 a fadin jihar. Ya kara da cewa yanzu haka shirye-shiye sun yi nisa wajen kara samar da asibitoci a jihar da kuma shirin daukar manya da kananan malaman asibiti a fadin jihar.

Ya ce an dauki mutum dubu 10 a kananan hukumomi da kauyukan jihar, wadanda suke bai wa hukumar lafiya labarin bullar cuta.

Daga karshe ya ce gwamnati za ta samar da allurar rigakafin sankarau wadda za a yi wa yara ’yan kasa da shekara daya.