Kasar Indonesiya ta amince da wani sabon kundin manyan laifuka da ya tanadi haramta saduwa tsakanin maza da mata matukar ba su yi aure ba.
Sai dai sauyin dokokin ya jawo ce-ce-ku-ce ainun, inda wasu ke kallonsa a matsayin wani yunkuri na tauye ’yancin watayawa a kasar da ke yankin Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya.
- ‘Yan Najeriya miliyan 25 za su fuskanci karancin abinci a 2023 — Rahoto
- An Kashe Mata Da Mayaka 55 A Rikicin ISWAP Da Boko Haram
Sabuwar dokar dai ta shafi ’yan asalin kasar ne da ma bakin da ke zaune a cikinta, sannan kuma ta dawo da haramcin zagin Shugaban Kasar da manufofin kasar da ake kira da Pancasila.
Majalisar Dokokin Kasar dai ta amince da sabon kundin da murya daya a ranar Talata, kuma zai maye gurbin wanda aka jima ana amfani da shi tun bayan samun ’yancin kan kasar a shekarar 1946.
A baya dai, Indonesiya na amfani da kundin da ya kunshi wasu daga cikin dokokin kasar Jamus ne da na al’adun kasar wadanda ake kira da ‘hukum adat’, da kuma dokoki na zamani na kasar.
Gabanin kada kuri’ar amincewa da sabon kundin, Ministan Shari’a na kasar, Yasonna Laoly, ya shaida wa ’yan majalisar cewa, “Mun yi iya bakin kokarinmu wajen saka muhimman batutuwa da kuma mabanbantan ra’ayoyi bayan an tafka muhawara.
“Sai dai lokaci ya yi da za mu kafa tarihi mu fitar da sabon kundinmu ta hanyar yin fatali da wanda muka gada daga Turawan mulkin mallaka,” inji Ministan.
Sai dai sabbin dokokin sun ci karo da zanga-zanga daga kungiyoyin dalibai a duk fadin kasar lokacin da aka fitar da kwafin daftarinsu a watan Satumban 2019, inda daliban suka ce suna cike da fargabar za a rika take hakkokinsu da ita.
Sai dai kafin sabon kundin ya zama cikakkiyar doka, dole sai Shugaban Kasar ya rattaba masa hannu, kamar yadda Mataimakin Ministan, Edward Hiariej, ya bayyana.
Kazalika, ba nan take za a yi fatali da tsohon kundin a fara aiki da sabon ba, har sai nan da shekaru uku masu zuwa.