Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Wakiali takardar bukatar amincewarta da karin kasafin N894bn domin sayen makamai da allurar rigakafin COVID-19.
Takardar neman amincewar da Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Talata ta ce karin kasafin ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman bukatu.
- Ban ga dalilin barazanar tsagerun Neja Delta ba — Buhari
- Yadda ’yan ta’adda ke ribibin dibar ’yan bindiga a matsayin mambobinsu
Sauran bukatun kuma za a sanya su a cikin kasafin shekarar 2022, wadda ake sa ran gabatarwa a watan Satumba, 2021.
Ta ce karamin kasafin zai tabbatar da samar da makamai da sojoji za su yi amfani da su wajen samar da tsaro.
Ragowar kuma za a yi amfani da su domin tabbattar da ganain an yi wa kashi 70% na ’yan Najeriya da suka cancanta allurar rigakafin COVID-19, daga yanzu zuwa shekarar 2022.