✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kare Muhalli: An kaddamar da murhun gas na girki dubu 34 a Katsina

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka yi bikin kaddamar da murahun girki dubu 34 masu aiki da iskar gas tare da dashen itatuwa…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka yi bikin kaddamar da murahun girki dubu 34 masu aiki da iskar gas tare da dashen itatuwa a Jahar Katsina.

Bikin kaddamarwar wadda Ministan harkokin mata ta tarayya Dame Pauline K. Tallen tayi a sakatariyar karamar hukumar Rimi a karkashin kulawar ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Katsina bisa jagoranci Kwamishinan ma’aikatar Hajiya Rabi Muhammad Daura.

Kamar yadda Ministan ta ce, an kawo murahun ne domin rarrabawa a kananan hukumomin 34, a inda kowace karamar hukuma zata samu murhu dubu daya don rarrabawa mata domin kawo masu sauki a wajen dafuwar abinci.

“Kamar yadda aka sani, mata suna wahala sosai a wajen dafuwar abinci musamman ta irin yadda hayaki ke cika masu idanu wanda hakan na jawo masu matsalar ciwon idanu”

Kazalika, tun farko sai da Kwamishinar harkokin mata ta Jahar Katsina Hajiya Rabi ta ce, yin amfani da murhun zai kawo sauki hatta ga magidantan da kuma lafiyar iyayen gidan, kana ma ma’aikatarta zata ci gaba da wayar da kan mata akan yin amfani da kuma yadda za’a rika amfani da wadannan murahu kana ta gode ma su da su ci gaba da dashen itatuwa domin kare muhallinsu.