✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kare mai tsoro

Wani kare ne ya je gidan wani malami domin  a ba shi lakani. Ya ce wa malam: “Ina son a ba ni asirin yadda zan…

Wani kare ne ya je gidan wani malami domin  a ba shi lakani. Ya ce wa malam: “Ina son a ba ni asirin yadda zan kama mazuru cikin sauki.” Malam ya ce masa to ya saurare shi. Suna nan zaune sai ga kura ita ma ta zo zauren malam ta zauna da tata lalurar. Kafin malam ya saurare ta, sai ya waiwayi kare, ya ce masa: “Me ke matsalarka? Sake bayyana mini.” Shi kuwa kare da ya ga kura sai ya ce: “Allah gafarta malam, yanzu lakanin yadda zan koma gida lafiya nake so!”