✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karamar Sallah: Gwamnati ta bayar da hutun Talata da Laraba

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar da hutun ranakun Talata 4 ga watan Yuni da Laraba 5 ga watan Yuni 2019 don gudanar da bikin karamar…

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar da hutun ranakun Talata 4 ga watan Yuni da Laraba 5 ga watan Yuni 2019 don gudanar da bikin karamar Sallah.

Sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gidan Najeriya Barista Georgina Ekeoma Ehuriah, ce ta sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, wanda Daraktan watsa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Mohammed Manga, ya sanyawa hannu.

Ta kuma sanar da sakon taya murna ga musulman kasar akan kammala azumin watan Ramadan ta yi fatan an gudanar da bukukuwan sallah lafiya.