Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce kar ’yan Najeriya su yi tsammanin ganin gagarurin sauyi farat daya a bangaren tsaro daga sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro.
NEF ta ce kwazo da nasarar Hafsoshin Tsaron sun danganta ne da irin muhimmacin da Shugaban Kasa kuma Babban Hafsan Tsaron Kasa ya ba wa bangaren ya kuma shiga a yi da shi.
- Yadda ’yan bindiga suka karkashe juna a Katsina
- Za a jibge sojoji mata 200 don sintiri a hanyar Abuja-Kaduna
- Yadda ’yan bindiga suka karkashe juna a Katsina
- Yadda za a kara hasken fata cikin kankanin lokaci
“Sabbin Hafsoshin za su fi samun kwarin gwiwa idan Babban Hafsan Tsaon Kasa ya shiga cikin sha’anin ana damawa da shi yana kuma bibiyar abubuwan da suke yi,” inji Kungiyar.
Daraktan Yada Labaran NEF, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya kuma shawarci Shugaban Kasa da ya guji nesanta kansa da harkokin tsaro kasa, sannan ya rika kama kwamandojin tsaro da laifi a duk lokacin da suka gaza.
“Dole Shugaba Buhari ya rika bibiyar sha’anin tsaro a-kai-ak-kai, sannan ya rika dora alhakin gazawa ko nasarar da aka samu a kan kwamandoji da shugabannin tsaron,” inji shi.
Dokta Hakeem, ya gargadi Hafsoshin da kar su ba da kunya ga ’yan Najeriya da ke da kyakkyawan fata a kansu na shawo kan matsalolin tsaron da suka dabaibaye kasar.
“A yanzu da kasar nan ke fama da tsoffi da sabbin kalubalen tsaro, ya kamata sauyin Hafsoshin Tsaro ya zama wata alama cewa Shugaba Buhari ya amince ya bukatar yin muhimmin sauyi a bangaren tsaro da bunkasa karfin Najeriya na kare kasar da mutanen cikinta.
“Duk da cewa an yi canje-canjen a makare, ’yan Najeriya na ganin amsa kiran da suka yi ta yi ne na sauya shugabannnin tsaro a matsayin daga daga cikin hanyoyin kawo kwarewa da kara karsashi da nagartar shugabancin rundunonin sojin kasar nan.
“Kungiyar na kiran ’yan kasa kar su rudu da tunanin cewa sauye-sauyen nan za su kawo gagarumar sauyi a nasarar da aka samu kan kalubalen tsaro a kasar nan,” inji shi.
Ya kara da cewa sabbin hafsoshi, “Suna daga cikin rundunar sojin da ta fi shekara 10 tana fama da matsalar tsaro na ta’addanci da sauransu. Hanya daya da za su ba wa ’yan Najeriya kwarin gwiwa shi ne su ninninka a kan nasarorin wadanda suka gada.
“Abin da ya kamata Hafsoshin su fi ba wa muhimmanci su ne: inganta kwarewar aikin soji, kara wa dakaru azama da karsashi da kuma yakar almundahana a aikin soji.
“Sun san yadda muka damu kan rashin makaman zamani da suke fama da shi da kuma yadda kungiyoyin cikin gida da kasashen waje ke sukar yadda suke aiwatar da yaki da ta’addanci.
“Yana kuma da kyau su yi shugabancin da zai samar da kwarewa da kiyaye dokokin aikinsu,” inji shi.