Hukumomin tsaro a Jihar Kano sun ba da tabbacin samar da isasshen tsaro, musamman a yayin gudanar da taron Maulidin Ɗariƙar Tijjaniyya, domin ganin an yi an kammala cikin aminci.
Rundunar ’yan sandan jihar ta bayar da wannan tabbacin ne bayan ɓullar rahotannin da ta ce na nuna cewa ’yan ta’adda sun shirya kai hari a jihar.
Amma a safiyar Asabar, kakakin ’yan sanda a Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanar cewa, rundunar da sauran hukumomin tsaro sun tashi haiƙan domin tabbatar da isasshen tsaro, musamman a lokacin Maulidin.
Ya kuma buƙaci jama’a da su kasance masu lura tare da ankarar da jami’an tsaro game da ayyukan ɓata-gari ko wani motsi da ba su aminta da shi ba.
“Jami’an tsaro sun fito domin tabbatar da ganin an yi ‘Maulud’ lafiya an gama lafiya. Saboda haka a lura sosai da ɓata-gari. Duk masu shirin kawo barazana Allah (SWT) Ya yi mana maganinsu. Sai a taya mu da addu’a,” kamar yadda ya walla a shafinsa na Facebook.
Hakan na zuwa kamar mi’ara koma baya ne, bayan da farko rundunar ta kai samame tare da umartar masu shirya taron na ranar Asabar su dakatar da shi.
A ranar Juma’a rundunar ta sanar cewa ta samu rahoton shirin ’yan ta’adda na kai hari a jihar, don haka ya buƙaci mutane su kauce wa wuraren taron jama’a.
A ranar ne jami’an rundunar suka je zauren taron da aka shirya gudanarwa a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, suna neman wa watse.
Amma daga bisani Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Abdullahi Waiya, ya fitar da sanarwar cewa babu makawa sai taron ya gudana.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba ta sa labarin wata barazanar tsaro, don haka babu dalilin dakatar da taron ko tunanin mugun abu zai faru a wurin taron wanda aka shafe shekaru 39 ana gudanarwa duk shekara da mahalarta daga duk faɗin Najeriya kuma an cika ka’idoji wajen shirya shi bana.
Daga nan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta janye jami’an tsaron daga harabar taron.