✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano Pillars ta sake rikitowa daga teburin Firimiyar Najeriya

Sunshine Stars ta lallasa Kano Pillars da ci daya mai ban haushi.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sake rikitowa da ga saman teburin gasar Firimiyar Najeriya da ake fafatawa a bana.

Pillars ta yi gamo da cikas ne yayin da Sunshine Stars ta doke ta da ci daya mai ban haushi yayin haduwarsu ranar Lahadi a wasan mako na 32.

Sadeeq Yusuf ne ya jefa wa Sunshine Stars kwallon da ta samu maki uku a  wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon, Pillars ta koma mataki na hudu a teburin gasar da maki 55, daidai da na Rivers United da take mataki na uku, wacce ta samu nasarar doke Warri Wolves da ci 2-1 yayin karawarsu a ranar Lahadin.

Ita kuwa Nasarawa United wacce ta tunkude Pillars daga mataki na biyu a makon da ya gabata, tana nan a matakin dai duk da maki 55 duk da shan kashin da ta yi a hannun Ifeanyi Ubah United yayin haduwarsu a wasan mako na 32.

Akwa United ta ci gaba da jan ragamar gasar da tazarar maki biyar bayan nasarar da ta samu a kan Enyimba International da ci 1-0 a gida.

Ga sauran sakamakon wasannin mako na 32 da aka buga ranar Lahadi:

  1. Abia Warriors 2 – 1 Kada City
  2. Enugu Rangers 2 – 1 Wikki Tourists
  3. Lobi Stars 1 – 0 Adamawa United
  4. Mountain Of Fire And Miracles 0 – 0 Katsina United
  5. Ifeanyi Ubah 2 – 1 Nasarawa United
  6. Jigawa Golden Stars 1 – 0 Plateau United
  7. Akwa United 1 – 0 Enyimba International
  8. Rivers United 2 – 1 Warri Wolves