Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sake rikitowa da ga saman teburin gasar Firimiyar Najeriya da ake fafatawa a bana.
Pillars ta yi gamo da cikas ne yayin da Sunshine Stars ta doke ta da ci daya mai ban haushi yayin haduwarsu ranar Lahadi a wasan mako na 32.
Sadeeq Yusuf ne ya jefa wa Sunshine Stars kwallon da ta samu maki uku a wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Da wannan sakamakon, Pillars ta koma mataki na hudu a teburin gasar da maki 55, daidai da na Rivers United da take mataki na uku, wacce ta samu nasarar doke Warri Wolves da ci 2-1 yayin karawarsu a ranar Lahadin.
Ita kuwa Nasarawa United wacce ta tunkude Pillars daga mataki na biyu a makon da ya gabata, tana nan a matakin dai duk da maki 55 duk da shan kashin da ta yi a hannun Ifeanyi Ubah United yayin haduwarsu a wasan mako na 32.
Akwa United ta ci gaba da jan ragamar gasar da tazarar maki biyar bayan nasarar da ta samu a kan Enyimba International da ci 1-0 a gida.
Ga sauran sakamakon wasannin mako na 32 da aka buga ranar Lahadi:
- Abia Warriors 2 – 1 Kada City
- Enugu Rangers 2 – 1 Wikki Tourists
- Lobi Stars 1 – 0 Adamawa United
- Mountain Of Fire And Miracles 0 – 0 Katsina United
- Ifeanyi Ubah 2 – 1 Nasarawa United
- Jigawa Golden Stars 1 – 0 Plateau United
- Akwa United 1 – 0 Enyimba International
- Rivers United 2 – 1 Warri Wolves