Kungiyar Kano Pillars ta haye saman teburin gasar Firimiyar Najeriya bayan ta lallasa Enyimba International da ci 2-1 a wasan mako na 25 da suka fafata ranar Lahadi.
Yayin haduwar tasu, Enyimba ce ta fara zura kwallo a ragar Pillars ta hannun Victor Mbaoma kuma haka sakamakon ya kasance har aka tafi hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa ne Kyaftin din Pillars, Rabi’u Ali ya farke mata a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Yayin da ya bai wuci saura minti 15 a tashi daga wasan ba, Pillars ta kara kwallo ta biyu ta hannun Ifeanyi Eze da hakan ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.
Da wannan sakamako ne Pillars wacce take bani in baka wajen jan ragamar teburin Firimiya Najeriya a bana da Akwa United, yanzu ta koma ta daya a makon nan.
A yanzu Pillars ta hada maki 48 kenan cikin wasanni 25, yayin da ita kuwa Akwa United ta samu maki daya bayan ta tashi 2-2 a gidan Wikki ranar Lahadi.
Ga yadda sakamakon mako na 25 da aka buga ranar Lahadi a gasar Firimiyar Najeriya ya kasance:
Abia Warriors 1-1 FC IfeanyiUbah
Adamawa United 0-2 Plateau United
Dakkada FC 0-1 Lobi Stars
Heartland FC 2-2 Rivers United
Kano Pillars 2-1 Enyimba International
Rangers International 1-1 MFM FC
Katsina United 2-1 Nasarawa United
Kwara United 3-0 Jigawa Golden Stars
Warri Wolves 2-1 Sunshine Stars
Wikki Tourists 2-2 Akwa United