Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya amince da nada Lionel Emmanuel Soccoia, dan kasar Faransa a matsayin sabon kocin kungiyar Kano Pillars.
Kocin ne zai jagoranci kungiyar zuwa gasar Confederation Cup ta Nahiyar Afirka a kakar badi da za a fara.
Nadin nasa ya biyo bayan dokar Hukumar Kwallon Afirka, CAF na cewa duk kungiyar da za ta shiga gasar Afirka, dole mai horar da ita ya mallaki lasisin CAF matakin ‘A’ ko kwatankwacinsa.
Hakan ya sa tsohon kocin kungiyar, Ibrahim Musa wanda ke da lasisin a matakin ‘C’ da ‘B’ ba zai iya jagorantar kungiyar ba a gasar.
Kakakin Kano Pillars, Alhaji Idris Malikawa, ya ce sabon kocin zai sauka a Kano a Laraba, 21 ga Oktoba, inda zai sanya hannu a takardar kwantiragin fara aiki.
Lionel Emmanuel Soccoia, wanda ya horar da kungiyoyi a kasashen Afirka irinsu Kamaru da Afirka ta Kudu da Zambiya da sauransu, zai sanya hannu a kwantiragin shekara daya ne.