Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta bayyana neman dan wasanta, Sunday Chinedu ruwa a jallo.
Kakakin kungiyar, Rilwanu Idris Malikawa Garu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Litinin.
Rilwanu ya ce tun da farko dai Mashawarcin kungiyar, Lionel Soccio ne ya ba dan wasan hutun kwanaki hudu domin ya ziyarci iyalansa amma yanzu tsawon makonmni biyu kenan bas u ji duriyarsa ba.
Ya kuma ce har yanzu dan wasan bai sanar da inda ya shiga ba.
“Shugaban kungiyar, Shu’aibu Surajo ya ba dan wasan wa’adin kwanaki ya dawo ko ya fuskanci hukuncin horo mai tsanani.
“Muna iya kokarinmu wajen kare martaba da walwalar ’yan wasanmu, amma hakan ba ya nufin za mu lamunci halin rashin da’a daga gare su ba,” inji Rilwanu.
Daga nan sai ya ja kunnen ’yan wasan kan su kara jajircewa wajen fuskantar kalubalen dake gaban kungiyar.