✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano ce kan gaba a sabbin masu kamuwa da Coronavirus a Najeriya

A cikin kwanaki biyu, jihar Kano ta kasance a sahu na gaba a yawan sabbin masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya. Alkaluman Hukumar Yaki…

A cikin kwanaki biyu, jihar Kano ta kasance a sahu na gaba a yawan sabbin masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya.

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Juma’a an samu mutum 238 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasar, kuma 92 daga cikinsu a jihar ta Kano suke.

Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa, “Zuwa karfe 11.00 na daren 1 ga watan Mayu, mutum 2,170 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Bayan mutum 92 da aka samu a jihar Kano, an kuma samu 36 a Yankin Babban Birnin Tarayya, 30 a Legas, 16 a Gombe, 10 a Bauchi, takwas a Delta, shida a Oyo, biyar a Zamfara da Sakkwato, hudu a Ondo da Nasarawa, da kuma uku a Kwara, da Borno, da Edo, da Ekiti, da Yobe, sai biyu a jihar Adamawa.

Yayin da  jihohin Imo, da Ebonyi, da Ribas, da Enugu  ke da mutum daya ko wacce.

Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 351 bayan sun warke, yayin da mutum 68 suka riga mu gidan gaskiya.

Jihar Kano ta kasance kan gaba a yawan sabbin masu kamuwa da Coronavirus tun daga ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu zuwa lokacin da Hukumar ta NCDC ta fitar da kididdigar ta ranar Juma’a.