Wasu mutum 10 ’yan uwan juna sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kaduna zuwa Kachia a yayin da suke dawowa daga daurin aure a Jihar Kano.
Hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Litinin, bayan motarsu ta yi karo da wata motar ice.
- NAJERIYA A YAU: Muna So A Yi Zaben Gwamnoni Lafiya – ’Yan Najeriya
- Ganduje ya shirya wa zaben Kano makarkashiya —NNPP
Wani mazaunin Kachia, Isiyaku Musa Kachia, ya shaida wa Aminiya cewa, dukkan wadanda suka rasu Kanawa da ke zaune a garin Kachia.
Ya ce: “Sun je garinsu Kano ne daurin aure, a hanyarsu ta konawa Kachia, motar Golf da suke tafiya a ciki ta yi karo da wata babbar motar ice, su 10 da ke cikin motar duka suka mutu nan take.”
Ya ce an yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Kachia.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kaduna, Zubairu Mato, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya danganta hatsarin da tsinkewar birki.
Ya ce motar kirar Golf ta yi lodi fiye da kima a lokacin da hatsarin ya auku, kuma daga cikin wadanda abin ya shafa akwai maza manya takwas da yara maza biyu.