✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan hukumomin kaura da Kachiya sun yi taro kan rikicin makiyaya da manoma

A ranar Alhamis din makon jiya ne aka gudanar da taro a tsakanin Fulani makiyaya da manoma da sauran masu ruwa-da-tsaki kan harkokin tsaro ta…

A ranar Alhamis din makon jiya ne aka gudanar da taro a tsakanin Fulani makiyaya da manoma da sauran masu ruwa-da-tsaki kan harkokin tsaro ta yadda za a inganta zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a yankin Kudancin Kaduna.

An gudanar da taron ne a kananan hukumomin kaura da Kachiya, inda aka gudanar da taron yankin kaura a dakin taro da ke kofar Fadar Kagoro, kuma an gudanar da shi ne musamman kan batun mace-macen shanu da aka yi a yankin, inda ya samu halartar Shugaban karamar Hukumar kaura Mista Zitung Basahuwa Agog da Kwamishinan kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kaduna Farfesa Kabir Mato wanda Babban Sakataren Ma’aikatar ya wakilta.

A jawabin Mista Zitung Basahuwa Agog, ya ce lamarin mace-macen shanun ba abin a kawar da kai ba ne domin a cewarsa, ba za su bari a sake kawo musu wata fitina a yankin ba, kuma hakan ne ya sa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya bai wa lamarin muhimmancin da ya dace don kawar da duk wani abu da zai zama barazana ga zaman lafiya a yankin.

Farfesa Kabir Mato, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar kananan Hukumomi da Masarautu, Malam Adamu Mansur da ya jagoranci wakilan gwamnati daga Ma’aikatar Gona da kwararru masu bincike, ya bayyana muhimmancin da zaman lafiya ke da shi a cikin al’umma sannan ya tunatar da manoma da makiyaya irin tsohuwar kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, sannan ya yi kira a gare su da su kiyayi duk wani abu da zai shiga tsakaninsu.

kwararrun likitocin dabbobin sun debi samfuri daga ciyayi da ruwa da kashin dabbobin da jininsu da kayan ciki da sauran abubuwa guda 36 saboda su je su yi gwaje-gwaje a kai domin gano hakikanin abin da ya haddasa mutuwar shanun.

Tun farko a lokacin da yake jawabi, Shugaban kungiyar Ci-gaban Mutanen Kagoro (KDA), Mista Benjamin Gugong ya nuna takaici da mamaki kan mace-macen shanu masu yawa a dan kankanen lokaci wanda hakan ke neman haddasa fitina a yankin. Ya yi kira ga kowane bangare da ya maida wukarsa kube a jira sakamakon binciken kwararru da za su yi gwaje-gwaje a kai domin gano ko guba aka sanya wa dabbobin ko wata annoba ce daban, sannan idan guba ce, wacce iri ce kafin fuskantar mataki na gaba.

A garin Kachiya da ke karamar Hukumar Kachiya ma an gudanar da irin wannan taro a karkashin dukan kungiyoyin kabilun Kachiya domin ci gaba da zaman lafiya da juna musamman ganin yadda damina ta fara a yankin.

Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Malam Yusuf Usman Garba ya ce an shirya taron ne musamman don makiyaya da manoma inda ya jinjina wa mahalarta kan yadda suka nuna goyon bayansu ga batun zaman lafiya. A lokacin da take jawabi, Shugabar Riko ta karamar Hukumar Kachiya, Hajiya Zulai Rabi’u Ja’afaru, wadda Muhammad dahiru Tanko ya wakilta, ta yi kira ga jama’ar karamar hukumar su ci gaba da zama jakadun zaman lafiya tare da aiwatar da duk wani abu da zai kawo ci gaban karamar hukumar.

Mai martaba Sarkin Kachiya (Agwom Adara), Malam Maiwada Galadima, wanda Moses Stephen ya wakilta, kira ya yi ga jama’ar masarautar su rika lura da dukan bakin da ba su yarda da su ba a cikinsu don shaida wa hukumomin da abin ya shafa. A karshe ya jinjina wa jama’ar masarautar a kan zaman lafiyar da aka samu inda ya umarce su da su ci gaba da rungumar juna.