✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin RIBY na hankoron ‘yan Najeriya miliyan 1.5 don bude musu asusu

Kamfanin Hada-Hadar Kudade na RIBY Finance Life Technologies Limited, da ke tallafa wa kungiyoyin ’yan kasuwa da kananan rance, zai taimaka wajen inganta samun rance…

Kamfanin Hada-Hadar Kudade na RIBY Finance Life Technologies Limited, da ke tallafa wa kungiyoyin ’yan kasuwa da kananan rance, zai taimaka wajen inganta samun rance tare da ajiyar kudi a banki, ga ’yan Najeriya ta hanyar inganta rajistar masu sha’awar shiga ta intanet.

Kamfanin zai yi amfani da wani gangami mai taken: ‘Riby 1.5 Million’ wajen taimaka wa kungiyoyi da kuma al’ummomi don samun damar ajiya a banki; inda za su samu kudin ruwa daga ajiyar, bayan wani lokaci.

Babban Jami’i, kuma wanda ya kafa Kamfanin, Salami Abolore ya ce: “Mun mayar da hankali ga rukunin ’yan kasuwar da aka bari a baya; amma wanda ke da matukar muhimmanci a nan gaba. Muna hankoron samar wa abokan huldarmu damar samun kudade masu yawa a rayuwa da kyakkyawar ajiya don gobe tare da samun damar mallakar gidaje. Muna bai wa wadannan ababuwa uku fifiko, sakamakon su ne ginshikan karfin tattalin arziki.”

Ya ce kungiyoyi na da muhammancin gaske a Najeriya, dan haka dole kasar ta maida hankali sosai a kansu; domin rage radadin talauci a kasar nan.

Kamfanin zai kaddamar da ayyukansa ne a jihohi 10, daga shiyyoyin kasar nan shida; kuma za su dauki kananan ’yan kasuwa da masu fasahar kirkire-kirkire a wurare daban-daban na kasar nan. Jihohin sun hadar da Kano da Kogi da Binuwai da Oyo.