A ranar Laraba Rukunin Kamfanin Yada Labarai na Media Trust, mai wallafa jaridun Daily Trusta da Aminiya da Saturday Trust da Trust TV, zai karrama ma’ikatansa da suka nuna bajinta a aikinsu.
Ma’aiaktan da za a karrama sun hada da wadanda suka yi bajinta a bakin aikinsu da wadanda suka cika shekara 10, 15 da kuma 20 suna aikin a kamfanin sai kuma gwarzayen ma’aikata da masu rikon amana.
- Sarkin Hadeja ya bukaci karin tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa a Jigawa
- DAG LARABA: Yadda Abincin Dan Adam Ke Iya Zama Guba
Ma’aikata sama da 35 ne dai za a karrama a wani kasaitaccen biki da kamfanin ya shirya domin nuna godiya da jinjina gare su tare da nuna su ga duniya, a hedikwatar kamfanin da ke Abuja.
Janar-Manaja Mai Kula da Harkar Ma’aikata ta Kamfanin Media Trust, Hadiza Ibrahim Bala ta bayyana wa Aminiya cewa kan fara wannan karramawar ne kusan shekara 15 da suka gabata.
Ta ci gaba da cewa, “Abu ne wanda shugabanni masu hannun jari a kamfanin suka kirkiro tun kafin na fara aiki da wannan kamfanin, bayan sun ga ya cancanta duk wani ma’aikaci da ya ba da kwazo da basira a yadda yake bada gudunmawa ga kamfanin Media Trust kuma har ya kai har shekaru shekara 10 zuwa sama.
“To tabbas duk wanda ya kai wannan lokacin kamfani zai karrama shi da farin cikinsa bisa yadda kullum yake iya kokarinsa wajen kokarin ganin kamfanin ya bunkasa, shekara ba daya ba, har goma sha.
“Ai wannan ba karamin abu ba ne duk wanda ya yi hakan ya kamata a karrama shi ka nuna farin cikinka da irin gudunmawar da ya bayar.
“Kuma wannan an fara shi mu muna dorawa ne kan a bin da muka tarar ana yi, kuma muna kokarin mu canza kan yadda zamani ke tafiya da ilimi.
“Kullum muna amfani da tunani sababbi na ilimin kimiyya da kuma yadda za mu bunkasa abin yadda zai yi kyau sosai, kuma na wannan shekarar muna fatan zai yi kyau sosai da samun ci gaba a cikin shirye-shiryen namu.
“A kwanakin nan da muke tattaunawa da shugabanninmu sun nuna cewa, kullum ana dada kawata abin ne, kuma nan gaba ba wai dole sai ma’aikatan kamfanin ba, abokan huldarmu wadanda muka san sun bunkasa mu suna taimakon mu wajen tafiyar da harkar kasuwancinmu, irin wadannan za mu iya cewa wane-da–wane ga irin gudunmawar da suke kawo mana, su ma idan irin wannan ya taso za mu iya gayyatar su mu karrama su, mu ba su wata kyauta na cewa mun gode da abin da kuke mana.
“A bangaren ma’aikata na yi maganar a kan wadanda suka yi shekara 10 da shekara 15 da wadanda suka yi shekara 20 za a karrama.
“Ban da su akwai wasu kuma wadanda aka yi tunani tun da can, na manyanmu duk wanda ya zama gwarzo a harkar aikinsa yana jajircewa, to shima ana tsayawa ba wai a zaba kawai ake yi ba.
“Muna zama a matsayinmu na shugabannin Kamfanin nan mu fito da sunayen mutane, wani lokacin ana iya samun sunayen mutane kamar biyar daga kowane bangare-bangare.
“Amma za mu zauna ne a matsayinmu na manya mu tantance kuma mu tabbatar mun yi abu tsakani da Allah, daga nan sai a fitar da gwarzon nan. Yawanci ana cewa mutum biyu wadanda suka jajirce wato gwarzaye ke nan.”
Kyautar Hazaka da Rikon Amana
“Sannan kuma akwai bangaren (Integrity Award) na ma’aikacin da yake aiki bisa amana; Duk wadannan karramawar Gwarzo da na Amana abubuwa ne da Kamfaninmu ba ya wasa da su.
“Saboda da haka wanda yake ya nuna rikon amana kuma wasu za ka ga sun samu kansu ne a wani hali, ba tare da saninsu ba kamar ana gwada su ne, ba tare da sun sani ba.
“Amma sai ka ga mutum ya danne zuciyarsa bai son zuciya ba kuma ya tuna cewa aiki yake yi a bisa amana, kuma ko yaya za a kawo wani abu don a yaudare shi, ko kuma a sa shi ya yi wani abu da bai kamata ba, sai ya rike gaskiyar nan ya yi abin da ya san ya kamata.
“Irin wannan ba ma sa sani sai daga baya a ce ai a lokaci kaza abu kaza ya faru kuma, an zata wane zai abin amma sai ya bada mamaki ya yi abin da ya cancanta su ma irin wannan rukunin ma’aikan muna karrama su a wannan rana.
Yada karramawar za ta kara wa sauran ma’aikata kwarin gwiwa
“A bangaren aikinmu akwai abin da ake cewa (staff retention) yana nufin wasu hanyoyi ne da ake bi na gyara wajen aikinka, inda shi kansa ma’aikaci ba ma ya son ya ce shi zai tafi, zai zauna ya dade maka ya dade shekara da shekaru saboda yana jin dadin wurin da yake aiki.
“Wadanda suka shekara hudu zuwa biyar a Kamfanin, suka ga cewa wane ya yi shekara goma an yi gagarumin biki an zo an nunawa duniya irin shekarun da ya yi yana aiki, wani abu ne da kowa zai yi sha’awa.
“Sai ka ji yana cewa, nima ina fatan Allah Ya nuna min wannan shekarun ni ma a yi min irin wannan.
“A shekarun baya yadda ake yin sa ba a ma kawata shi ba, amma a ’yan shekarun nan mun kawata abin, babban biki ake yi kuma mutum ya ga cewa an wallafa hotonsa a gaban jarida, saboda wadanda suka samu wannan karramawar za a wallafa su don duniya ta gan su.
“Tabbas yana taimaka mana ma’aikata ka ga su ma burinsu su zauna su yi wannan shekaru kamar yadda ’yan uwansu suka yi.
“Saboda haka abu ne mai kyau, ma’aikatun da ba sa irin wannan ya kamata su yi koyi don idan sun yi za su ji dadi.”