✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Facebook ya fara amfani da harshen Hausa

A farkon makon nan ne kamfanin Facebook ya sanya harshen Hausa a cikin jerin harsuna da masu mu’amala da shafinsa za su iya amfani da…

A farkon makon nan ne kamfanin Facebook ya sanya harshen Hausa a cikin jerin harsuna da masu mu’amala da shafinsa za su iya amfani da shi.
Kafar sada zumuntar wanda take da jama’a masu amfani da ita akalla guda biliyan daya da miliyan 800 a duniya baki daya, ta ce ta dauki matakin ne saboda yadda ta fahimci cewa akwai dimbin masu amfani da harshen wadanda suke shiga shafin a kullum.
Sai dai ko gabanin fara amfani da harshen, shafin Facebook yana amfani da harsunan Afirka kamar: Kiswahili da Afrikaans da Af-Soomaali da Malagasy da Tamazight da sauransu.
Kodayake ba kamfanin Facebook ba ne na farko a cikin jerin manyan kamfanonin sadarwa na duniya da ya ba da damar amfani da harshen, idan aka yi la’akari da yadda kamfanin Google (wato shafin matambayi ba ya bata) ya dade da samar da hakan.
A karon farko a watan jiya ne, wani karamin jirgi mara matuki ya tashi sama a birnin Arizona na Amurka, a wani mataki na burin kamfanin Facebook na samar da intanet ga miliyoyin mutane a yankuna masu wuyar kaiwa. Tsarin shi ne jirgin mai aiki da hasken rana, zai yi shawagi a sama na wasu watanni, yana samar da intanet ga mutane a doron duniya don su samu ikon shiga shafinsa.
A halin yanzu dai kamfanin shi ne na bakwai a sahun manyan kamfanonin duniya ta fuskar karfin tattalin arziki.
A farkon bana ne kamfanin ya bayyana samun ribar Dala miliyan 701 a watanni ukun karshe na shekarar da ta gabata.