✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kambama kwalliyarki da ‘ya’yan itace

Ko kun san cewa duk abubuwan da suka kunshi ‘ya’yan itatuwa na da muhimmanci wajen gyaran jiki? Idan ba ku sani ba, sai mu ce…

 Ganyen Aloe VeraKo kun san cewa duk abubuwan da suka kunshi ‘ya’yan itatuwa na da muhimmanci wajen gyaran jiki? Idan ba ku sani ba, sai mu ce muna yi muku albashir din akwai ‘ya’yan itatuwa ko kwallonsu da ke kambama kwalliyar mace ko namiji. Don haka ne a wannan makon muka kawo muku yadda ake amfani da ‘ya’yan itatuwa wajen gyaran jiki, musamman ma wadanda suke son magance matsalar fata, ko masu son muryasu ta yi zaki.
Domin zakin murya:
Za a samu ganyen mangwaro, sai a tafasa shi, sannan a rika sha kullum, hakan zai taimaka murya ta yi zaki. Akwai matan da suke da katuwar murya da idan sun yi magana sai a yi tsammanin namiji ne, to idan suka yi hakan za su samu murya mai zaki. Za a iya shan wannan ruwan sau biyu ko uku a rana.
Domin kunar fata:
A samu kwallon dabino kamar 10 sai a gasa su, sannan a daka har su zama gari mai laushi. Bayan haka, a samu man kwakwa a hada da garin kwallon dabino, sai a rika shafawa a wurin da aka kone.
Domin magance furfura:
A daka ganyen kori da na aloe bera da kuma na lalle. Bayan haka sai a shafa a gashi mai furfura, sannan a  wanke bayan minti 30. Yana da kyawu a rika amfani da wannan hadin kamar sau 3 zuwa 4 a mako.
Domin samun fata mai laushi:
A nika nutmeg, sai a hada shi da madara, sannan a shafa a jiki kullum kafin a yi wanka. A bari ya bushe a fatar jiki kafin a wanke. Yin hakan kullum na sanya fata laushi da yalki da kuma damshi.