A cikin wani gida da ke kusa da Rafin Karas a Unguwar Rikkos da ke Karamar Jos ta Arewa wata mata ce mai suna Kaka Malama, mai kimanin shekara 35.
Gidan nata zagaye yake da wani rufin kwano. Amma abin mamaki, shi ne akalla mata 10 masu ciki ne suke ziyartar wannan gida duk mako don ta musu aikin juya ciki.
Mata masu cikin sukan ziyarci matar a kowane lokaci ba dare, ba rana, domin ta taimaka musu su haihu ba tare da an yi musu tiyata (CS) a asibiti ba.
Aikin wannan mata shi ne juya ciki ya dawo daidai musamman ma idan har dan da za a haifa a juye yake. Malama Kaka ta kware wajen yin wannan aiki, kuma mata na tururuwa zuwa wajenta don su samu biyan bukata.
A binciken da Aminiya ta yi ta gano cewa mata masu ciki daga Kano da Kaduna da Sakkwato har ma daga Abuja sukan zo wurin Malama Kaka don ta yi musu aikin juya ciki su haihu ba tare da an yi musu tiyata ba.
Daya daga cikin wadanda ke taimaka wa Malama Kaka mai suna Mariya Ibrahim ta ce baiwa ce Allah Ya hore wa Kaka Malama, inda a kasa da minti 30 sai ka ga ta juya cikin.
Mariya ta ce, “Cikin mitin 30 za ka ga ta juya ciki, kuma babu wani zafi da mai cikin za ta ji, mai ciki za ta ji dan bambanci a lokacin da take aikin juya cikin, daga ta kammala sai ta kama hannun mai cikin ta taba cikinta da shi, don ta tabbatar da cewa cikin ya koma yadda ya kamata ya kasance, daga nan za ta bukaci mai cikin ta je asibiti don a tabbatar da cikin ya koma yadda ya kamata.”
Malama Kaka wadda ta samu lakabin ‘Kaka’ daga wurin kakarta ta ce ta koyi aikin juya ciki ne a wurin kakarta, ta kuma girma ne a wurin kakarta da ke Unguwar Gangare da ke birnin Jos.
Ta ce, “Sunan kakata Hauwa’u amma yawancin mutane suna kiranta Kaka Malam, ana kirana Malama saboda da matsalar da nake da ita (ta nakasa), inda mahaifana suka kai ni asibitoci don a yi mini aiki a kafata amma abin ya ci tura, wani Bature ma ya taba fada wa mahaifana cewa babu wani abu da za a yi mini in warke, shi ne sai ake ce mini Malama.”
Ta bayyana cewa ta fara taimaka wa kakarta a lokacin da take da shekara 15, inda “Ta koya mini yadda zan fahimci wurin da kai da hannuwa da kuma kafofin jaririn da ke ciki suke,’ inji ta.
Ta ce, “Ina shekara 18 aka yi mini aure, daga nan sai na ci gaba aikin sosai, saboda wannan aikin gadonsa muka yi a wurin kakanni, domin kakata ta yi gadon ne daga wurin mahaifinta da ke Biu a Jihar Borno.”
Yawaicin yadda take yin aikin na gargajiya ne, amma Kaka Malama ta ce takan tilasta wa mata masu ciki su je asibiti don a yi musu gwajin hoto (ultrasound) kafin ta yi musu aikin juya cikin.
“Ko a lokacin da nake da cikin dan autana na je asibiti, a nan na gane cikin ya juye, to bayan na je asibiti sai suka ce za su kwantar da ni, sai na ce musu surukata ta taba mutuwa a lokacin da za a yi mata aikin tiyata (CS), sai na ce musu zan koma gida, da na dawo gida ne sai na juya cikin da kaina, sannan na koma asibiti na haihu,” inji Kaka Malama.
Kaka ta ce takan fara aikin ne bayan ta yi Bismillah, “Sannan sai in ci gaba da taba cikin don gane inda kan jaririn yake, sannan a hankali sai in rika tattaba cikin ina juya cikin har sai ya koma daidai. Sannan in kama hannun mai cikin don ta taba ta tabbatar da cewa cikin ya koma daidai. Daga nan akwai magungunan gargajiya da nake ba mai ciki inda za ta rika sha a kunu ko shayi, ana samun wadannan magungunan ne daga Maiduguri,” inji ta.
Ta ce kamar yadda kakarta ta koya mata, ita ma ta koya wa ’yarta mai suna Hauwa wannan aiki na juya ciki, inda a yanzu take wannan aiki ita kadai.
Ita kuwa Hauwa cewa ta yi, “Na taso na ga kakata da mahaifiyata suna yi, don haka gado ne, kuma ina jin dadin wannan aikin taimako da nake yi duk da cewa ana samun na kashewa.”
Hauwa ta kara da cewa a yanzu tana shirye-shiryen karatun aikin ungozoma don hakan ya kara ba ta damar yin aikin juya cikin ba tare da an samu matsala ba.
Hauwa ta ce kakarta ta rasu kimanin shekara hudu da suka gabata, amma mahaifiyarta, wato Kaka Malama ita ce wadda mata masu ciki suka fi ziyarta kan batun juya ciki a birnin Jos.
“Mata masu yawa da suka hada da dukan addinai da yaruka sukan zo wurinmu musamman masu cikin da aka bayyana musu cewa cikin ya juye don haka sai dai a yi musu aikin tiyata, inda nan da na za ka ga sun zo wurinmu,” inji ta.
Kaka Malama ta ce ba ta taba samun wata matsala ba tunda ta fara aikin juya cikin fiye da shekara 18 domin duk matar da ta yi wa aiki kowace ta haihu lafiya.
“Nakan karbi Naira dubu takwas ga wadanda suke zaune a Jos, inda nake karbar Naira dubu 10 a wurin wadanda ba mazauna Jos ba, wadanda suke Jos sukan iya zuwa wurin kusan sau uku, amma wadanda suke wajen Jos sau daya suke zuwa kafin su haihu,” inji ta
“Akwai lokacin da mutane suke cewa za su biya ni amma ana kammala musu aiki to ba za ka sake ganinsu ba, akwai masu zuwa ma su ce mini su ba su ba matansu damar zuwa wurina don a yi musu aiki ba, amma akwai wadanda suke fada wa mazansu amma idan aiki ya yi kyau sai ka ga sun ki biya kuma,” inji Kaka Malama.
Ta bayyana cewa wani abin da takaici shi ne yadda wadansu mata suke amfani da sunanta wajen ha’itar mutane a Jos.
“Akwai wata yarinya da take cewa ita jikar kakata ce, inda take gwada aikin juya cikin, amma dai a karshe dole suke dawowa wurina saboda yarinyar ba ta ma san abin da take yi ba,” inji ta.