✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kai tsaye: Realmadrid ta cire Juventus

Abin da za mu iya kawo muku ke nan a wannan wasa. Da fata kuna jin dadin yadda muke kawo muku labarin wannan wasa kai…

Abin da za mu iya kawo muku ke nan a wannan wasa. Da fata kuna jin dadin yadda muke kawo muku labarin wannan wasa kai tsaye?

Juventus ta yi waje. Real Madrid ta tsallaka zuwa wasan kusa da na karshe. An ta magana a kan penaty da aka ba Madrid. Ko dai sun cancanta ko ba su cancanta ba, yanzu dai canjaras. Juventus ta fita.

Ronaldooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooooo….. Madrid ta zura ta a zaren Juventus… Shi ke nan… Juventus sai kuka.

Ronaldo zai buga. S’an Madrid ya zo a mintin karshe…

Penalty…. n ba Madrid Penalty…

An kara minti uku.

87:  Saura minti  3 kacal

81: Saura minti 9.  Madrid 0 Juventu 3.

75: An canja Modric, inda Kovacik ya shigo

70: Saura minti 20. Filin Bernabeu na cikin rudu yanzu haka. Madrid na neman kwallo daya domin su samu kwanciyar hankali

64: Juventus sun samu wani irin natsuwa. Yanzu idan aka tashi haka za a kara lokaci. Ko za a tashi haka?

60: Goaaallllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllllll: Juventus ta ci na uku… 3 da 3 ke nan

59: Huguaannnnnnnnnnnnnnnnn………… Ayyyaaaaa. Navasa ya tsare

51: Har yanzu dai ana ta tirka tirka. Juventus 2 Madrid 0

An canja Bale da Caseiro, inda Lucas da Asensio suka shigo filin.

Mun dawo. Yanzu an dawo fili domin a ci gaba da goge raini.

An je hutun rashin rabin lokaci. Juventus na cin Madrid 2 da nema. Amma saura kiris Varane ya zura kwallo a ragar Juventus, inda ya yi rashin sa’a kwallon ya bugi sandan post. Sai an dawo za mu sha kallo

41: Juventus 2 Realmadrid 0. Jimilla ya zama Realmadrid 3 Juventus 2. Da sauran  aiki har yanzu a gaban Juventus. Ko za su karasa aikin? sai dai an gama kawai

Realmadrid na rashin Ramos a wannan wasa. Rashinsa ya nuna a fili a bayansu. Dukan kwallayen guda biyu, da kai aka ci.

37: Goaaallllllllllllllllllllllllllllllllllllll: Mandzukic ya kara na biyu. Juventus 2 Realmadrid 0.. Lallai yau fa akwai kallo.

2: Goaallllllllllllllllllllllllllllll…… an dara fa.. Mandzukic ya jefa kwallon farko a ragar Realmadrid a minti biyu da farawa..

#AnFara…..

‘yan wasan sun shigo fili. Yanzu za a fara. Yau ma fa akwai kallo.

‘Yan banchin Juventus: Juan Cuadrado, Claudio Marchisio, Kwadwo Asamoah, Wojciech Szczesny, Daniele Rugani, Stephan Lichtsteiner, Stefano Sturaro.

 

JUVENTUS (4-3-3): Gianluigi Buffon; Mattia De Sciglio; Mehdi Benatia, Giorgio Chiellini, Alex Sandro; Sami Khedira, Miralem Pjanic, Blaise Matuidi; Douglas Costa, Gonzalo Higuain, Mario Mandzukic. 

‘Yan benchin Real Madrid : Karim Benzema, Kiko Casilla, Theo Hernandez, Lucas Vazquez, Marcos Llorente, Marco Asensio, Mateo Kovacic.

‘Yan wasa:

REAL MADRID (4-3-1-2): Keylor Navas; Daniel Carvajal, Raphael Varane, Jesus Vallejo, Marcelo; Luka Modric, Casemiro, Toni Kroos; Isco; Gareth Bale, Cristiano Ronaldo.

Yau ne za raba gardama tsakanin Realmarid da Juventus a zagaye na biyu a wasan kwata final na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a filin wasa na Barnabeu.

Wannan wasan ne wasa na 21 da kungiyoyin nan guda biyu za su buga. Realmadrid ta lashe sau 10,  Juventus ta lashe 8, sannan aka yi kunnen doki sau biyu.

Hakanan kuma Realmadrid ta zura kwallo a duk wasannin guda 24 da suka gabata kafin wasan yau, inda suka zuwa kwallaye 63.

Sannan a duk wasannin da Juventus da suka buga Realmarid a gidan Realmadrid din guda 10, sau biyu kawai suka ci Realmadrid a gida, suka yi kunnen doki sau daya, sannan aka doke su sau 5.

A wane bangaren kuma, Ronald ya zura kwallon waannin day a buga da Juventus sau shida, inda yake da kwallaye 9 a ragarta. Kuma ba taba samun wani dan kwallo bad a ya ci kungiya daya sama da haka. Messi ma ya ci Arsenal sau 9, sais hi Ronaldo din da ya kuma ci Bayern Munich 9. Sai kuma yau idan ya kara, zai zama na goma.

A wasan karo na farko, Realmadrid ta doke Juventus da ci 3 da nema. Ko yau Juventus za ta farke? Abin ba a cewa komai domin jiya Roma tab a Barcelona mamaki. Ken an kawai sai an tashi. Ku biyo domin samun labarin wasan kai tsaye.