✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafin a hana shigo da taki

A cikin makon da ya gabata ne aka ruwaito Ministan Tsare-tsare kuma mataimakin shugaban Hukumar Tsare-tsare ta kasa, Dokta Abubakar Sulaiman yana bada shelar cewa…

A cikin makon da ya gabata ne aka ruwaito Ministan Tsare-tsare kuma mataimakin shugaban Hukumar Tsare-tsare ta kasa, Dokta Abubakar Sulaiman yana bada shelar cewa gwamnatin tarayya za ta bullo da wata manufa da za ta tabbatar da an daina shigo da Takin zamani daga kasashen waje. Ministan ya fadi haka ne, lokacin da ya kai wata ziyarar bin sawu a Kamfanin yin Taki na kasa da ke Kaduna, Kamfanin da ke cikin Kamfanonin da gwamnatin tarayya ta cefanar a shekarun baya ga `yan kasuwa.

Wata sanarwa da aka ba manema labarai a Abuja daga ofishin Ministan ta ruwaito Minista Dokta Sulaiman yana cewa “Akwai bukatar mu daina shigo da dukkan wani nau`in kayayyakin da za mu iya yi a cikin gida, ciki kuwa har da takin zamani. Wata sanarwa da za ta fayyace manufofin gwamnatin tarayya na nan tafe cikin `yan makonni masu zuwa, da za su kula da haka. Duk abin da za mu iya yi a cikin kasar nan, to, lallai mu daina shigo da shi.” In ji Ministan Tsare-tsaren. Kamfanin yin Takin zamanin na kasa da ke Kaduna yana iya yin tan 70,000, na takin duk shekara, amma a lokacin da gwamnatin ta cefanar da shi tan 5,000, kacal yake iya yi a shekara, saboda sakaci irin na rashin kula` da kayayyakin gwamnati da ake fama da shi a kasar nan.
Ba ko shakka wanda duk ya san irin siyasar da ake fama da ita akan samar da Takin zamani ga manoman kasar nan duk shekara, musamman manoma za su yi maraba da jin wannan aniya ta gwamnatin tarayya, don idan har gwamnatin ta daina shigo da takin, to, kuwa za ta samar da wata hanyar ingantacciya, wadda ta fi ta yanzu wajen ganin manoman suna samun takin wadatacce kuma akan lokaci a kasar nan. Don kuwa a yau manoman da kyar da jibing goshi kuma a makare suke samun takin a kodayaushe
Rabon takin na cikin-manyan batutuwan da gwamnatin tarayya ta PDP take tutiya da shi, kuma har ta sanya shi cikin batutuwan yakin neman zaben bana, inda ta kan fadawa `yan kasa cewa sabon tsarin rabon takin zamanin da ta bullo da shi, shi ne na raba takin ta yin amfani da wayar hannun manoma. A karkashin shirin an sai wayoyin hannu na Naira biliyan 6, da aka rabawa wasu manoman kasar nan a farkon bullo da shirin, wanda ta wannan hanya ce, gwamnatin ta ce tana raba wa manoman takin, bayan sun biya kudadensu.
Tsarin rabon takin da gwamnatin tarayyar ta ke tutiyar ta kashe cin hanci da sauran magudi da suke tattare da rabon takin zamanin kasar nan, alhali gwamnatin ta manta da cewa wannan tsari ba abin da ya rage wa manoma a cikin irin bakar wahalar da suke saba sha, kafin su samu takin duk shekara, kuma ai ita gwamnatin ta kwan da sanin cewa batun samar da takin zamanin ba shi kadai batun da ya addabi manoman kasar nan cikin harkokin noma.
Alal misali, duk da wannan tsari da gwamnati take tutiyar ta bullo da shi, har gobe ba wani manomi da ya ke samun wadataccen takin zamanin da ya ke bukata kuma akan lokacin da ya kamata a kasar nan. Koda wannan sabon tsarin rabon taki ta wayar hannu da gwamnatin ta bullo da shi, har yanzu kome girman gonar manomi bai wuce a aiko mai da sakon ya je ya karbi buhu biyu ba, walau a lokacin noman damina ko na rani kuma takin ba zai zo hannunsa ba tsakanin watan Afrilu zuwa na Mayu, lokacin noman damina kenan, har sai daminar ta yi nisa a tsakanin watan Yuli da na Agusta, bayan ya sayi na kasuwa mai dan Karen tsada. Hakazalika idan lokacin noman rani ne kamar yadda ake ciki yanzu, to, shi ma maimakon a ce tun a cikin watan Nuwamba zuwa na Disamba, takin ya je hannun manoman, amma sai ka tarar takin mahukunta ba za su tashi rabon takin ba, sai wajejen irin wannan lokaci na watan Fabrairu zuwa na Maris, kamar dai yadda ake samun rahotanni yanzu. Ya Ilahi ina harkokin noma zasu inganta a irin wannan tsari.
Ba wai batun samarwa da manoma taki ingantacce kuma akan lokaci kadai ke matsalolin da suke kawo koma baya, ba akan harkokin noma a kasar nan ba, a`a akwai batutuwa na rashin samun sauran kayayyakin ayyukan gona, irin su tantan din noma da iri dan wuri da wadatattun Malaman gona da za su rinka nusar da manoma dabarun noma na zamani da rashin samun basussukan ayyukan gona masu sauki, kuma akan kari da kuma uwa uba farashi ingantacce da kasuwar amfanin gonar a daidai kakar kowane amfanin gona.
Mai karatu zai ga makalar tawa ta yau ta fi ba da karfi ne akan batun takin zamanin, saboda irin yadda Ministan Tsare-tsaren ya ce shi gwamnatin tarayya take kokarin ta bullo da wata manufa akansa da aniyar ganin ma ta daina shigo da shi, sannan taka kokarin karawa da wasu kayayyaki da kasar nan za ta iya yinsu a cikin kasa. Wannan babbar magana ce, gwamnati ta ce za ta hana shigo da wasu abubuwa da ake iya yi a cikin gida, lokacin da kofofin kasar nan suka dade a bude, ta yadda komai shigo da shi ake sasakai ba kaidi, wannan ta sanya kusan dukkan masana`antu a rufe.
Akan batun hana shigo da takin zamani ina ga wannan shi ya fi komai sauki, idan har gwamnatoci da Hukumominsu, irin na Cibiyoyin binciken ayyukan gona da kungiyoyin kasa da kasa masu taimaka wa manoman kasar nan da hikimomi da dabarun noma irin na zamani irin su Sasakawa Global 2000 ta tsohon shugaban kasar Amurka Mista Jimmy Carter suka dukufa ka-in da-na`in, ba bu abin da zai gagara. Don Masana fannin ayyaukan gona sun tabbatar da cewa daga sharar gona irin su sassabe da sarar karmo da tushiya da sauran sharar gona irinsu kara da karmami da muka taso muka ga iyayenmu suna tarawa daga karshe su kona, da yin amfani da kashin dabbobi da sharar gidajenmu, manoma za su iya samarwa da kansu takin ingantace da ba ya kona kasa kamar yadda ake kukan takin zamani yana yi kuma akan lokaci. Bayan wannan akwai mu da shara damfare a kauyukanmu da biranenmu, musamman a manya birane, sharar da masanan suka ce za a iya sarrafata cikin sauki ta zama taki mai amfani ga dukkan ire-iren amfanin gonarmu, kuma wadatacce da za a rinka samu cikin gida ba wahala kuma mai rahusa.
Don haka, kafin akai ga hana shigo da takin zamanin, akwai bukatar gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da Hukumominsu, lallai su maida hankali wajen tallafa wa hukumomi da ma`aikata da na ambata a sama, ta yadda bincike akan sarrafa sharar gari da ta gonaki za a iya sarrafa su zuwa takin. Yanzu kuma shi ne lokacin, don ko ba komai aikin gonar nan dai shi ne makomar kowace kasa ba man fetur ba.