✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafa labin Shanu ne kawai zai magance rikicin makiyaya da manoma a jihohin Benuwai da Nasarawa – Al-Makura

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta aiwatar da aikin kafa labin shanu a filayen da gwamnatinsa ta…

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta aiwatar da aikin kafa labin shanu a filayen da gwamnatinsa ta bayar da gudunmawarsu don kafa labin shanun don kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da takwarorinsu manoma da ya ki ci ya ki cinye wa a jihar.

Gwamnan ya gabatar da bukatar ne a wajen wani gagarumin taron masu ruwa da tsaki akan rikicin da ke tsakanin fulani makiyaya da manoma a jihar wanda gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar Kwamitin Shugaban Kasa kan rikicin fulani makiyaya da manoma suka shirya aka gudanar a hotal din Ta’al dake Lafiya a karshen mako da ya gabata.

Gwamna Al-Makura wanda kwamishinan ma’aikatar Kananan Hukumomin jihar, Alhaji Haruna Osegba ya wakilce shi ya bayyana bukatar da akwai na gwamnatin tare da hadin kan Gwamnatin jihar su tabbatar da aiwatar da aikin kafa labin shanun, su kuma bai wa kungiyoyi masu zaman kansu da sauran al’umma baki daya damar kafa labin shanun don kiwon dabbobi a jihar ba tare da an samu matsala ba.

Ya ce a kokarin da gwamnatinsa ke yi na rage ko kawo karshen rikici da tabbatar da zaman lafiya a jihar baki daya tuni a cewarsa Gwamnatinsa ta kafa wata kungiya ta musamman wace zata rika sasanta rigirgimu tsakanin al’ummomin biyu musamman a yankunan karkara da sauran kananan Hukumomin jihar baki daya.

A cewarsa mutane da dama sun yi asarar rayukansu sakamakon rikicin manoma da fulani makiyaya mafi muni daya auku kwanakin baya a garuruwa da kauyuka dake iyakokin jihar da makwabtarta Benuwai inda a cewarsa aka kuma yi asarar dukiyoyin miliyoyin Naira. Ya kara da cewa, sai da gwamnatinsa ta gina sansanin ’yan gudun hijira sakamakon rigimar inda a cewarsa a yanzu kimanin ’yan gudun hijirar 250,000 daga jihohin biyu suna zaman hijira. Ya ci gaba da bayyana cewa “Ina so in yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta bayar da gudunmawar jami’an tsaro daga Abuja zuwa wadannan kauyuka a lokacin da hakan ba shakka ya taimaka wajen kawo karshen rikicin.”

Tun farko a jawabin sakataren kwamitin da shugaban kasa ya kafa don magance rikici, Mista Andrew Kwasari ya bayyana cewa, masu ruwa da tsaki sun sake zama kwanakin baya sun bullo da wasu hanyoyi da dabarun magance matsalar inda ya ce daga cikinsu akwai bukatar Gwamnatin jihar Benuwai ta kara wa’adin tattaunawa da fulani makiyaya akan kafa labin shanun a jihar da tallafawa tare da inganta harkokin wannan kwamitin sasantawa da kirkiro da doka da zai hana kananan yara yin kiwo a cewarsa shi kansa dabbobi na ci wa manomi amfanin gona. Sauran yarjejeniyar da aka cimma a yayin zaman, a cewarsa sun hada da a rika gudanar da kidayar makiyaya ’yan asalin jihar dana dabbobinsu don a iya gano su daga cikin makiyaya baki da sauransu.

Game da tsaro kuwa sakataren ya bayyana cewa an bukaci duk hukumomin tsaro a jihar su rika aiki tare da su kuma su rika magance matsala akan lokaci kafin ya yi muni. A cewarsa an kuma bukaci gudumawar kungiyoyin ’yan banga a wadannan wurarai don taimakawa jami’an tsaron. Haka kuma ana son bangaren Sarakunan gargajiya an bukace su, ne su rika taimaka wa jami’an tsaro da ingantattun bayyanai da zasu taimaka wajen dakile ayyukan bata-gari su kuma rika shirya tarurrukan zaman lafiya wa al’ummominsu akai-akai da sauransu. Taron ya samu halartar duk Hukumomin tsaro a jihar da mambobin kwamitin shugaban kasa kan rikicin da Sarakunan gargajiya da kungiyoyin manoma daban-daban da na fulani makiyaya da kungiyoyin addinai daban-daban da jami’an gwamnati da sauransu.