✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kada Kuri’a Ta Fi Ibada —Jarumin fim

Fitaccen jarumin fim a masana’antar Nollywood Anayo Modestus (Kanayo O Kanyo) ya ce fitar ’yan Najeriya domin yin rajistar zabe ya fi musu alheri a…

Fitaccen jarumin fim a masana’antar Nollywood Anayo Modestus (Kanayo O Kanyo) ya ce fitar ’yan Najeriya domin yin rajistar zabe ya fi musu alheri a kan zuwa wuraren ibada.

Jarumin ya bayyana hakan ne ta wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya ce duk wani dan Najeriya na da karfin ceto kasar daga halin da take ciki.

Amma sai ya yi amfani da makaminsa na rajistar zabe ta dindindin, wanda kuma ya ki yin hakan, to yana daga cikin wadanda ke haddasa wa kasar matsala.

Kanayo ya jaddada cewa zaben kansa ya fi zuwa coci ko masallaci saboda addu’a ko bata lokaci a kafafen sada zumunta ba su ne za su kai kasar ga ci ba, illa wannan zaben da za su fita su zabo wa kasarsu shugaba na gari.

Ya ci gaba da cewa, “Ni da kai muna da damar ceto kasarmu.

“Babu wanda zai iya yi mana hakan sai mu din.

“Kada ka ce kuri’arku ba za ta yi tasiri ba.

“Amma kafin komai, ka je ka sauke nauyin da ke kanka a matsayinka na dan kasa.

“Kar ku jahilci wannan maganar tawa ta zabe ya fi zuwa coci ko masallacin, domin addu’a ba za ta jefa kuri’a ba, mutane ne za su yi”, in ji shi.

“Idan don addu’a ne su ma gurbattau ai suna yi, masu babatu a kafafen sada zumunta kuma ai ba akwatin zabe a nan, abu ne na zahiri.

“Idan har yanzu ba ka yi rajistar zabe ta dindindin ba, to ka zama wani bangare na matsalar Najeriya. Ehe,” in ji Kanayo.

Jarumin wanda a yanzu ya zamo lauya, yana daga cikin fitattun mutanen da suka fito suka yi magana kan bukatar fitar ’yan Najeriya mallakar katin zaben na dindindin domin jefa kuri’a a zaben 2023 mai zuwa.

Sauran sun hada da  Falz, Mista Macaroni, Peter Okoye (P Square), Davido, MI Abaga (Mista Incredible), da sauransu.

Kanayo O Kanayo dai na daga cikin tsofaffin fitattun jaruman masana’antar fina-finan Nollywood da ya kwashe sama da shekara 20 ana jin amonsa.

Jarumin ya kuma yi fice bayan fitowa a fina-finai irin su ‘Lion Heart’ da kuma wani fim din da ya karbi kyaututtuka daban-daban har guda biyu.