✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kabilar Amish: Amurkawan da ba ruwansu da kayan kere-kere na zamani

An gano wata al’umma a Amurka da ba ta amfani da wutar lantarki da wayar hannu, kuma ba ta shiga mota. Wakilin Aminiya a Amurka…

An gano wata al’umma a Amurka da ba ta amfani da wutar lantarki da wayar hannu, kuma ba ta shiga mota.

Wakilin Aminiya a Amurka ya ziyarci daya daga cikn garuruwan da wannan al’umma take inda ya ce, wannan al’umma da ake kira da al’ummar Amish ana samunta a jihohi da dama a Amurka, sai dai ta fi yawa a Jihar Pennsylbania inda ya ziyarta. 

Ya ce inda rayuwar wadannan mutanen take da ban mamaki shi ne kayayyakin kimiyya da kere-kere na zamani da dama ne wadannan mutanen ba su amfani da su.

Da farko dai ba su shiga mota duk inda za su tafi suna da keken doki ne shi suke hawa kuma ba ka zuwa gidajensu ka ga suna amfanin da wutar lantarki, suna samun hasken da suke amfani da shi ne a gidajen su ta amfani da fitilar a-ci-bal-bal ko su samar da haske ta amfani da iskar gas.

Haka kuma ba a daukarsu hoto kuma ba su daukar hoton, wadannan mutanen sun ce ba su yarda da kere-keren zamani ba, a cewarsu suna tattare da kazanta da sabo. Kuma wadannan mutanen ba su karatun boko duk da yake suna da makaranta irin tasu, kuma a inda hakan ya yi musu wahala sukan bar yaransu su yi matakin karatu a matakin farko wato firamarr amma daga nan shike nan sai su fitar da su, su koya musu sana’ar da iyayen ke yi. Kuma wadannan mutanen ba su zuwa asibiti idan ciwo ya kama su.

Yawancin mutanen dai manoma ne kuma sun yi fice a harkar noma a Amurka, wannan ya sa da yawansu suka bunkasa kuma al’ummar ta kara fadada.

Da yawansu ba ka samunsu a cikin gari kuma bisa bayanai masu sahihanci an bayyana cewa wadannan mutane da zarar suka fahimci cewa wadansu jama’a sun fara yawa a inda suke zaune sai su tashi su koma inda suke zallarsu.

Bayanai sun tabbatar cewa wannan al’ummar ta fi yawa a jihohin Pennsylabania da Indiana da Ohio, kuma ana samunsu har a cikin kasar Kanada, kuma a yanzu ana samunsu a cikin jihohi 30 na Amurka.

Bayanai sun tabbatar da cewa wannan kabila ta Amish tana daya daga cikin al’umma mai saurin yaduwa, domin bayanai sun tabbatar da cewa wannan kabilar ta Amish tana da yawan jamaa da ya kai 5000 ne a 1920, amma adadin ya haura zuwa dubu 300,000 a yau.

Da yake wadannan mutanen ba shiga cikin jama’a suke yi ba, suna zama ne daga su sai su kashi 100 na ayyukan gonakinsu ’ya’yansu ne ke yi.

Kasancewa suna karuwa kuma ayyukan noman kadai ba za su iya rike su ba, ya sa suka fara surka wa da wasu ayyuka kamar sana’ar kafinta da suke tura ’ya’yansu su koya, sai kuma aikin gini, wani lokaci za ka same su a masana’antar sauran Turawa.

Sai dai gwamnatin Amurka ba ta kyale su ba wajen karbar haraji kuma an san su da bin doka da oda, sai dai kudin tallafi da gwamnatin Amurka take bai wa wanda ya bar aiki ko kuma mara aikin yi, ba su karban irin wannan kudin, domin suna kallon wannan kudin ko tallafi a matsayin kudin ruwa wanda bai halatta gare su ba.Wannan ya sa a wani lokai can baya wato a 1965 gwamnati ta cire su daga biyan haraji. Har yanzu a wasu jihohin da wadannan mutanen suke akwai daga cikinsu wadanda ba su karbar kudin tallafin da coci-coci ke bayarwa.

Wannan al’umma ba a taba samunsu cikin aikin kayan sarki, wannan ya sa gwamnati ba ta kula da daukar ’ya’yansu a wannan aiki, haka kuma ba su shiga harkokin siyasa ko na lauya.

Wadannan mutane sun haramta amfani da duk wani abu mai inji ko na’ura, misali talabijin da rediyo da kwamfuta, zuwa makarantar boko in ta wuce firamare.

A cewarsu ba wai suna kallon wadannan kere-keren ba ne a matsatsayin wasu miyagun abu amma kuma abubuwa ne da ka iya kai dan Adam ga ayyukan assha. Suna cewa amfani da wadannan abubuwa na iya sauya musu tunani ya sa su karbi wata bakuwar al’ada, kuma amfani da mota ko jirgi zai iya kawo rarrabuwarsu.

To sai dai kuma ana iya cewa akwai rudu cikn al’amarinsu domin kuwa sun yarda su shiga motar da wani zai tuka su amma ba dai su tuka da kansu.

Kuma da yake suna haihuwa da auratayya ne tsakaninsu kuma suna tsakiyar al’ummar da ake ganin ta waye sosai wannan ya sa wasu al’adun sun gurbata domin wadansu ’ya’yansu sun fandare suna yin duk abin da al’adun suka yi hani a yi, sau tari wadansu yaran ma da sun kai wasu shekara 15 zuwa 21 sai a tarar sun gudu sun bar iyayensu sun tsiri rayuwa irin ta Turawa tsantsa.

Wakilinmu ya ce ya ziyarci gonar daya daga cikin mutanen wannan al’umma inda suka je sayen nama amma sai ya ga kusan duk abin da suke amfani da shi a cikin gonar irin nasu ne da suka kaga ko suka samar da kansu. Wannan ne ya ja hankalinsa, ya so ya dauki hotonsu amma suka ce sam, sai dai ya dauki ta wajen mayanka kuma su ne ya hado da wannan labari.