✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki sun kashe ’yan bindiga 17 a Katsina

Jiragen Rundunar Sojin Sata ta Najeriya sun kashe ’yan bindiga 17 tare da tarwatsa sansanoninsu a Dajin Dunya na Jihar Katsina. Jami’in Yada Labaran Rundunar…

Jiragen Rundunar Sojin Sata ta Najeriya sun kashe ’yan bindiga 17 tare da tarwatsa sansanoninsu a Dajin Dunya na Jihar Katsina.

Jami’in Yada Labaran Rundunar Tsaro, Manjo Jana John Enenche ya ce jiragen rundunar “Operation Hadarin Daji” sun yi wa ’yan bindigar ruwan wuta ne a ranar Alhamis bayan samun bayanan sirri.

Enenche ya ce rundunar ta samu bayanai cewa ’yan bindiga masu alaka da kungiyar Ansaru sun yi sansani a dajin inda suke tara shanun sata.

Nan take a cewarsas aka tura jiragen yaki suka suka kuma yi nasarar halaka bata-garin da kuma tarwatsa maboyar tasu ma’ajiyarsu.

Ya ce daga baya bincike ya gano cewa an kashe ’yan bindiga sama da 17 baya ga wasu da dama da suka samu raunuka.

“Hedikwatar Tsaro na yaba wa sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Arewa maso Yamma saboda kwarewarsu, tana kuma rokon su da su kara azma domin kawar da ’yan bindiga”, inji shi.