✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jinjina ga Sarkin Gombe

A Najeriya, musamman a Arewa maso Gabas  kullum mata 1,549 ke mutuwa ta dalilin haihuwa a cikin kowace haihuwa dubu 100. Ke nan duk shekara ana…

A Najeriya, musamman a Arewa maso Gabas  kullum mata 1,549 ke mutuwa ta dalilin haihuwa a cikin kowace haihuwa dubu 100. Ke nan duk shekara ana rasa mata kimanin dubu 53 ta dalilin haihuwa.

Manyan dalillan da ke kawo wannan matsala; ba su wuce talauci da rashin asibitocin haihuwa da rashin asibitocin yara da rashin isassun malaman asibiti  da ungozomomi da sauransu ba. Abubuwan ne da ba su kamata a ce kasa, mai wadata irin Najeriya ba ta da su ba.

To  abin mamaki, abin takaici, duk da lalacewar harkar kwon lafiya daga matakin farko zuwa sama, sai ga shi a kasar nan ce ake kwashe kudin gwamnati a shirya zamba iri-iri.

In ban da wauta, ko rashin hankali, ta yaya, kai da ba ka da asibitocin haihuwa a garuruwa da kauyukan  jiharka, za ka kwashi miliyoyin Naira ka ba mawaka?

Ba ka da asibitocin haihuwa, amma ana ba ka Naira miliyan 500 duk wata a matsayin kudin ko-ta-kwana! Miliyan nawa za ta gina asibitin zamani na haihuwa a kauye ko unguwa? Da komai-da-komai bai wuce Naira miliyan 50.

Suna kiran kansu shugabanni, suna yaudarar talaka, amma har yanzu a kan jaki ake daukar masu juna biyu, a yi tafiya da su ta kilomitoci zuwa asibiti a wasu yankunan. Ka duba yadda mai juna biyu take, a ce kuma tana cikin nakuda, sannan a dora ta kan jaki, in da gata, kan babur a tafi da ita asibiti!

Dubi yadda wadansu masu dukiyarmu ke almubazzaranci da dukiya lokacin bikin aure ko suna. Rigar da amarya za ta sanya (Farar riga doguwa marar kyau, irin ta fatalwa) takan kai Naira miliyan daya. Rigar banza wadda daga ranar ba a kara sanya ta.

Wani auren sai a kashe sama da Naira miliyan 50, kudin da suka isa su gina babban asibiti na zamani a  kauye don a ceto rayukan dimbin iyayenmu mata.Amma aka watsa su a bikin auren da wani ko wata uku cikakku ana zaman amana ba za a yi ba.

Wadansu kan tafi kasashen Holland ko Faransa ko Jamus rainon ciki, can za a haifi dan ko ’yar a asibiti mafi tsada a duniya. Mutum ya kaso miliyoyin Naira, amma can gida a kasarsa, dimbin mata ne ke mutuwa saboda babu asibitin awon ciki a yankinsu. Wannan ya sa na jinjina wa Mai martaba Sarkin  Gombe, Alhaji Abubakar Shehu  Abubakar a kan namijin kokarin da yake yi na ganin an rage mace-macen mata masu juna biyu wurin haihuwa. Ba ji na yi ba, gani na yi da idanuna. Na je Gombe a kwanakin baya, kuma na ziyarci daya daga cikin asibitocin da Mai martaba ya gina, kuma abin ya burge ni matuka, domin asibiti ne dankarere na zamani wanda aka gina a tsakiyar unguwar talakawa. Asibiti ne da ya wuce raini, ya ma wuce irin wanda ’yan siyasarmu ke ikirarin ginawa  da sunan romon dimokuradiyya.

Asibiti ne ba aikin ha’inci, na zagaya ko’ina ciki da wajen asibitin kuma na yaba matuka.

Wani abin ban sha’awa game da wannan kokari na Mai martaba Sarkin Gombe, shi ne, ya ce  ba wani gangamin da za a yi wajen bude asibitin. Kawai nan da ’yan kwanaki asibitin zai fara aiki.

Wannan ya saba wa al’ada a Najeriya, inda ake tattaro mutane a nuna an yi wani abin kirki. Shi Mai martaba Sarki bai da irin wannan hali. Shi dai burinsa ya taimaki talakawa.

Mun zagaya sauran wurare inda za a kara gina wani asibitin, tunda kamar yadda aka tsara, za a gina ire-iren wadannan asibitoci da dama a Gombe.

Ba a harkar kiwon lafiya Sarki ya tsaya ba, akwai fannin ilimi, inda ya gina makarantun allo na zamani da dama a Gombe. Na ziyarci daya daga cikin irin wadannan makarantu mai suna Madarasatul Marhum, inda muka iske yara na ta karatu. Abin da ya ba ni  sha’awa shi ne, yaran ga sunan tsaf, sun yi wanka, kuma suna da kayan makaranta (yunifom), amma kuma da allo namu na gargajiya suke amfani wajen karatu. Na tattauna da malamin kuma shugaban makarantar Alaramma Malam Gambo, in da ya ce, makaranta tsohuwa de kuma dogon lokaci sun yaye dalibai sama da dubu 30. Cikin tsofaffin dalibansu har da wadanda suke karanta aikin likitanci a Jami’ar Maiduguri.

Ya ce mini, Mai martaba Sarki ne ke kula da duk bukatun yaran, ciki har da abinci da yunifom da sauransu. Kodayake, ba su hada karatun da na boko ba, amma sun sanya yaran da suka nuna sha’awar boko a makarantun boko. In lokacin boko ya yi, yaro zai tafi, idan ya dawo, ya dasa da na addini.

Wannan ba karamin namijin kokari Sarkin Gombe ya yi ba. Kamata ya yi sauran sarakunan Arewa, su yi koyi da shi a bangaren yin ayyukan jin kai. Ilimi da kiwon lafiya abubuwa ne da kai-tsaye suke inganta rayuwar talaka.

Abin ban haushi muna da attajirai a Najeriya, amma idan mutum yana yawo a kasar nan, yana ganin wahalhalun da talakawa ke ciki, sai ya dauka duk matalauta ne a kasar. Saboda an dauki rowa da keta an sanya a zukatan jama’a. Shi ya sa kasar ta ki ci gaba, tunda Allah ma Ya ce a yi zakka, a ciyar da marayu, a yi sadaka, a girmama bako, a yi alheri amma mutane sun yi watsi da wannan kiran. Suna tunanin Adam Smith shi ne zai samar musu da mafita. Shi ya sa ake ta wahala.

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talata ta Kasa

08165270879