✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jima’i: Guzurin bayanai ga matan aure (2)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka, muna fata kuna cikin koshin lafiya. Ga ci gaban makalar da muka fara kawo…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka, muna fata kuna cikin koshin lafiya. Ga ci gaban makalar da muka fara kawo muku a makon jiya. Muna fata za ku ci gaba da bin bayanin sau da kafa don cin ribar amfaninsa gare ku. Jan Hankali: Mun san wadansu za su yi zaton ko an yi amfani da kalaman da ba su dace ba, to muna sanar da su a bangaren da ya shafi batun aure musamman ma ta bangaren da ya shafi jima’i to babu batun kunya, bai kamata mata su boye abin da yake ransu da sunan suna jin kunya ba. A sha karatu lafiya.

 

Yin wasanni
Ba wai sai lokutan da za a sadu ba, ya kama ku rika yi wa mijinku wasanni a wadansu lokutan da kuka lura yana cikin nishadi. Za ku iya masa wasannin ne ta hanyar shafarsa, sosa gashin kansa, tattaba yatsunsa da lankwasa su, inda wani lokaci za ku rika zungurarsa kadan. Yana da kyau ku rika ba shi labarai masu ban dariya da sanya nishadi, wani lokaci ku rika zolayarsa, yanayin yadda zai rika sake jikinsa gare ku zai nuna muku yana samun gamsuwa. Ta wannan hanyar ma za ku iya isar da sakon nuna son jima’i ba tare da bayyanawa da baki ba.
Neman jima’i
A cikin kashi 100 kusan kashi 80 maza ne suke neman matansu idan aka zo batun jima’i, ina so mata su sani maza ba jin dadin hakan suke ba, sau da yawa nakan ji wadansu mazan na korafin hakan, sai dai idan sun bukaci matansu da batun jima’i ne suke amincewa. Maza suna so a ce matansu sun rika kirkiro hanyoyi daban-daban wajen isar da sakon son yayin jima’i, a lokuta da dama mata suna zama ne kawai ko da kuwa suna son jima’i, amma sai su yi gum har sai mijinsu ya bukaci hakan, wannan takan sanya namiji ya rika tunanin shi ne kawai yake son saduwa, sannan matansa babu ruwansu, hakan zai sa ya kasa samun ingantacciyar gamsuwa, ina so mata su fahimta ba wai zubar da maniyyi yana nufin gamsuwa yayin jima’i ba, a’a, samun gamsuwa a zuciya shi ne babbar gamsuwa.
Kalaman soyayya
Za ku iya kara wa jima’i armashi idan kuka rika yi wa mijinku kalaman soyayya, ko ku rika yi masa kirari, hakan zai sa ya rika jin dadi, inda kafin a ce wani abu ma sai ku ji ya samu gamsuwa, domin ita zuciya Allah Ya halicce ta da son kalaman da za su dadada mata, ta hanyar yi wa mijinku kalaman soyayya lokacin jima’i sai ku kara tasirantuwa a zuciyarsa har ya ji kun gamsar da shi ba tare da shan wahala ba. Kada ku yi zaton hakan kaskantar da kai ne, ba haka ba ne, yin wadannan kalaman zai sa mijinku ya rika jin kamar shi ne kadai namiji da ya rage a duniya.
Tausa
Bayan mijinku ya kai ga zubar da maniyyi wani abu da za ku yi masa don ya samu cikakkiyar gamsuwa shi ne, ku kankame shi a kirjinku zuwa wani dan lokaci, sannan ku rika yi masa tausassan kalamai a kunnensa, lokaci zuwa lokaci ki rika wasa a harshenki a kunnensa, a lokaci guda ki rika yi masa rada a kunnensa. Daga bisani ku rika yi masa tausa, za ku yi masa tausa ne a gabobinsa da kuma wuraren da suke motsa sha’awa. A yayin tausar za ku iya amfani da yatsunku ko harshenku wajen yin wasa a kwarin bayansa, kwarin dunduniyarsa da wuyansa da kuma kwarmin bayan kunnensa, wannan yana sanya maza nishadi da sakewa bayan an yi jima’i, hakan kuma zai ba shi cikakkiyar gamsuwa.
Ba jima’i muhimmanci
Wadansu matan suka nuna halin ko in kula a lokacin jima’i, to hakan na nakasa karsashin namiji wajen samun gamsuwa, kada ku nuna wa mijinku tamkar taimakonsa kuke yi yayin jima’i, Ku sadaukar da kanku, ku bayyana zautuwarku a lokacin da yake saduwa da ku, hakan zai ba shi gamsuwa ta hakika.
Bayyana sirri
Yana da matukar muhimmanci ku bayyana wa maigidanku sirrinku a bangaren jima’i, domin ta haka ne zai samu wani makulli da zai rika bude muku sha’awa har ya kai ga gamsar da ku, inda hakan ne zai ba shi damar samun cikakkiyar gamsuwa.
Za mu ci gaba

Domin karin bayani za ku iya tuntubar Bashir Liman ta wannan lambar 07036925654