✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jikan Sarkin Zazzau Shehu Idris Ya Zama Sabon Dan Isan Zazzau

Mahaifin sabon Ɗan Isan Zazzau, Marigayi Madakin Zazzau Aliyu Shehu Idris, shi ne babban ɗan arigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

Sarki Ahmed Nuhu Bamali ya tabbatar da naɗin jikan Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris a matsayin Dan Isan Zazzau.

Sabon Ɗan Islan Zazzau shi ne Alhaji Mustaph Aliyu Shehu Idris.

Mahaifin sabon Ɗan Isan Zazzau, Marigayi Madakin Zazzau Aliyu Shehu Idris, shi ne babban ɗan arigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

Sanarwa da mai magana da yawun Masarautar Zazzau Abdullahi Aliyu Ƙwarbai ya fitar ta ce naɗin Alhaji Mustaph Aliyu Shehu Idris a matsayin Dan-Isan Zazzau ya biyo bayan rasuwar baffansa ne, Ummar Shehu Idris, a ranar Litinin da ta gabata.