✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Jihohin Edo, Kaduna, Kuros Riba da Delta suna zawarcin daukar nauyin gasar a 2020

Yayin da ake sa ran rufe gasar wasanni ta kasa karo na 19 da take gudana a Abuja, tuni jihohin Edo da Kaduna da Kuros…

Yayin da ake sa ran rufe gasar wasanni ta kasa karo na 19 da take gudana a Abuja, tuni jihohin Edo da Kaduna da Kuros Riba da kuma Delta suka shiga zawarcin daukar nauyin gasar a shekara ta 2020.

Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ne ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba lokacin da ya halarci filin wasa na kasa da ke Abuja don ganin yadda gasar ta bana ke gudana.

Mista Solomon Dalung ya kara da cewa “Ganin  yadda gasar ta bana ta kayatar ya sa jihohi da dama suke zawarcin daukar nauyin gasar a shekarar 2020. Za mu tantance kuma mu darje jihar da za ta dauki nauyin gasar ta gaba, don kada a maimaita abin da ya faru a baya. Duk da an kwace gasar ce daga Kuros Riba aka mayar Abuja a bana, Jihar Kuros Ribas tana daga cikin jihohin da ke zawarcin daukar nauyin gasar a shekarar 2020 kuma idan ta cika ka’ida muka gamsu da shirin da ta yi, za mu iya amincewa ta dauki nauyin gasar ta gaba.”

“Kuskuren da aka samu game da Jihar Kuros Riba a baya shi ne, an ba jihar damar daukar nauyin gasar ta 2018 ce a lokacin da Gwamnan Jihar ke gab da sauka daga karagar mulki, amma wanda ya gaje shi sai ya yi biris da batun, hakan ya sa shirin daukar nauyin gasar ya rika tafiyar hawainiya, don haka muka kwace gasar muka mayar Abuja. Muna fatan irin hakan ba za ta sake faruwa a gaba ba,” inji Dalung.

A halin yanzu Gwamnatin Tarayya tana hada gwiwa ne da kamfanoni masu zaman kansu wajen daukar nauyin gasar ba kamar a baya ba da gwamnati ce kadai take daukar nauyin gasar.