Zuwa jiya Alhamis, jadawalin da Hukumar Shirya Gasar Wasanni ta Kasa karo na 19 a Abuja ta fitar ya nuna Jihar Delta ce ta farko bayan ta samu lambobin yabo 32 da suka hada da lambobin zinare 20 Da azurfa 4 da tagulla 8. Sai Jihar Ribas take ta biyu da lambobin yabo 23 da suka hada da zinare 5 da azurfa 7 da tagulla 11.
Sai Jihar Kano da ke matsayi na uku inda ta hada lambobin yabo 14 da suka hada da zinare 5 da azurfa shida da kuma tagulla uku.
Sai Edo ta hudu mai lambobin yabo 14 da suka hada da zinare 4, azurfa 4 da tagulla 6.
Sai Jihar Legas ta biyar da lambobin yabo 12 da suka hada da zinare 4 da azurfa biyu da kuma tagulla 12.
Sai Abuja ta 6 da lambobin zinare 3 da azurfa biyu da tagulla biyu.
Sai Jihar Bayelsa ta 7 da ta hada lambobin yabo 22 da suka hada da zinare 2, azurfa 14 da tagulla 6.
Sai Jihar Ondo ta 8 da ta samu lambobin zinare 2 kacal, ba ta samu azurfa da tagulla ba. Sai Jihar Oyo ta 9 da lambar zinare 1 da azurfa 5 da tagulla 6.
Ya zuwa jiya Alhamis kimanin jihohi 15 ne ba su samu lambar yabo ko daya ba.