Hukumar yaƙi da yaɗuwar cutar zazzaɓin cizon sauro (NMEP) ta bayyana Zamfara, Sakkwato da Kebbi a matsayin Jihohin da cutar ke cin karenta babu babbaka a Najeriya.
Kodinetan hukumar na kasa, Dokta Godwin Ntadom ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce Jihar Legas da Kwara ne jihohin da ke da karancin cutar malaria a halin da ke ciki a Najeriya.
Tun daga shekarar 2015 aka fara samun sauƙin cutar a ƙasar nan, sai dai abin mamaki shi ne jihohi 3 da ke Arewa maso Yammacin Najeriya abin karuwa yake yi.
- DAGA LARABA: Yadda Za Ku Yi I’itikafi Karɓaɓɓe
- Abin Da Ya Sa Ba A Cika Satar Ɗalibai Ba A Borno — Zulum
Ya ce yanayin samuwar maleriya a Najeriya ya ragu zuwa kaso 27 a 2015, ya kuma dawo kaso 22 a 2021, yayin da ake sa ran ya ragu sosai a wannan shekarar 2024, la’akari da ƙoƙarin da ake yi wurin yaƙi da cutar.
Ya ce, “Duk da ba mu yi watsi da tsoffin dabarun da muke amfani da su wurin yaƙar maleriya ba, mun bullo da sabbin dabaru.
“Muna samar da maganin zazzabin cizon sauro, muna rarraba gidajen sauro mai maganin kwari.
“Sannan kuma mun fara bayar da rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na lokaci-lokaci musamman a Arewacin kasar nan da zazzabin ya yi kamari, kuma mace-macen da ake samu a yankin ya ragu a sakamakon maganin da muke bayarwa.”
Dokra Ntadom ya ce kimanin mutane 608,000 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a faɗin duniya a shekarar 2022, kuma kaso 30 na adadin ‘yan Najeriya ne.
Ya ce, Najeriya za ta fara amfani da allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a bana daga jihohin Kebbi da Bayelsa kafin a faɗaɗa zuwa wasu sassan kasar.