A ci gaba da gasar wasannin motsa jiki na jihohin Kudu maso Yamma da ake gudanarwa a Jihar Legas, kungiyar kwallon kafa da ke wakiltar jihar Legas ta samu nasara a kan takwararta ta Jihar Oyo da ci 2-1.
Wasan wanda aka gudanar a filin wasa da ke unguwar Agege ya kayatar da ’yan kallo inda kowane kulob ya rika kai wa dan’uwansa hari.
dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jihar Oyo mai suna Tajudeen Sodik shi ya zura kwallaye biyu a ragar Jihar Legas amma daga bisani dan wasan Legas mai suna Michael Andrewa ya farke kwallo daya bayan an dawo rabin lokaci.
Haka ma kungiyar kwallon kafa ta Jihar Ogun ta lallasa takwararta ta Jihar Osun da ci 1-0 a wasan kusa da na karshe da suka buga.
Hakazalika a bangaren wasan daga nauyi kuwa tawagar jihar Legas ce ta zama zakara bayan da ta lashe tagulla a wasannin da aka gudanar a filin wasa da ke unguwar Yaba.
Jihar Oyo ta lallasa Legas a gasar wasanni ta jihohin kudu
A ci gaba da gasar wasannin motsa jiki na jihohin Kudu maso Yamma da ake gudanarwa a Jihar Legas, kungiyar kwallon kafa da ke wakiltar…